Wata Sabuwa: Gwamnatin Abba Ta Dauki Zafi kan Masu Taba Mutuncin Kwankwaso
- Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ce ba z ata lamunci taba mutuncin jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ba
- Ta gargadi magoya bayan Abba Gida-Gida su shiga taitayinsu domin duk wanda ya taba mutuncin Kwankwaso, zai fuskanci hukunci mai tsanani
- Wannan gargadi na zuwa ne yayin da siyasar Kano ke kara daukar zafi sakamakon ficewar Abba daga jam'iyyar NNPP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin jihar Kano ta gargadi magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su guji yin kalaman rashin ladabi ko taba mutuncin jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso,
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya fitar da wannan gargadi a ranar Litinin, a taron raba babura ga mambobin jam’iyya da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf na nan a wurin taron sa’ilin da aka bayar da wannan gargadi.
Gwamnatin Kano ta gargadi masu taba Kwankwaso
Sanusi Bature ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci da rashin da'a ko rashin mutunta Kwankwaso ba.
Ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoran siyasa wanda dole ne a mutunta matsayinsa a siyasar Kano, ba tare da la’akari da sauye-sauyen siyasar da ake ciki ba.
“Ba za mu lamunci rashin da'a ko taba mutuncin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ba. Duk wanda ya kuskura ya aikata haka zai fuskanci sakamako. Ba za mu taba amincewa da hakan ba,” in ji shi.
Shawarar da aka ba magoya bayan Abba
Ya bukaci magoya bayan gwamnan da su nuna natsuwa da girmamawa, musamman a wannan lokaci da ake samun takaddama a fagen siyasar jihar akano biyo bayan canjin da aka samu kwanan nan

Kara karanta wannan
Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso
A cewarsa, gwamnatin Kano ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin magoya bayanta, yana mai jaddada cewa kada sabanin ra’ayi na siyasa ya kai ga cin mutunci ko kalaman batanci.
Sanusi Bature ya kuma tunatar da magoya baya cewa mutunta shugabanni da bin doka a cikin tsarin siyasa su ne tushen zaman lafiya da gudanar da mulki na gari a jihar Kano.

Source: Facebook
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da mahawara bayan murabus din Gwamna Yusuf daga jam’iyyar NNPP, wani mataki da ya haifar da ra’ayoyi daban-daban a cikin tafiyar Kwankwasiyya.
Matakin da gwamnan Kano ya dauki hankali sosai, inda wasu suka mara masa baya, wasu kuma suka jaddada cewa suk wahala, suna tare da Kwankwaso, cewar Leadership.
Gwamna Abba ya kori hadiminsa daga aiki
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Sanusi Surajo Kwankwaso daga mukaminsa, kuma ya maye gurbinsa nan take
Mai magana da yawun gwamnan Kano , Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da haka yau Asabar, 24 ga watan Janairu, 2025.
Wannan na zuwa ne bayan Sanusi Surajo Kwankwaso ya sanar da cewa ya ajiye mukaminsa a gwamnatin jihar Kano, tare da tabbatar da cewa yana tare da Kwankwaso.
Asali: Legit.ng
