Sakon da APC Ta Fara Aika wa Gwamna Abba bayan Ya Fice daga NNPP

Sakon da APC Ta Fara Aika wa Gwamna Abba bayan Ya Fice daga NNPP

  • Ta tabbata gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya bayan dadewa ana jiran hakan
  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana cewa tana maraba da Gwamna Abba idan har ya yanke shawarar shigowa zuwa cikinta
  • Sakataren APC na jihar Kano, Ibrahim Sarina ya bayyana cewa kofar jam'iyyar a bude take ga Gwamna Abba tare da mukarrabansa

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf, bayan murabus dinsa daga NNPP.

Jam'iyyar APC ta bayyana fatan cewa nan ba da jimawa ba, gwamna wanda aka fi sani da Abba Gida Gida zai shiga cikinta a hukumance.

APC na maraba da Gwamna Abba zuwa cikinta
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Abba K Naisa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce sakataren jam'iyyar APC na jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso

Me APC ta ce kan Gwamna Abba Kabir?

Ibrahim Zakari Sarina ya amsa tambayoyi kan matakin siyasar da gwamnan zai dauka a gaba.

“Mun maraba da shi. Wannan ne kawai abin da za mu iya cewa a yanzu."

- Ibrahim Zakari Sarina

APC na fatan Gwamna Abba ya shigo cikinta

Ko da yake Gwamna Yusuf bai sanar a hukumance cewa zai shiga APC ba, Sarina ya ce jam’iyyar na da yakinin cewa nan ba da jimawa ba zai shigo cikinta.

Ibrahim Zakari Sarina ya jaddada cewa kofar APC a bude take ga Gwamna Abba tare da magoya bayansa.

“Ko da yake bai ayyana shigarsa APC kai tsaye ba, muna fatan nan ba da dadewa ba zai shigo APC. Kofarmu a bude take, kuma muna maraba da shi."

- Ibrahim Zakari Sarina

Sakataren jam’iyyar ya bayyana shigowar gwamnan a matsayin abin da ya kara wa APC karfi, yana mai cewa gwamnan na zuwa ne tare da adadi mai yawa na zababbun jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; An hango lam'a a ficewar Gwamna Abba daga NNPP

Wane tanadi APC ta yi wa Gwamnan Kano?

Ya kara da cewa tuni jam’iyyar ta dauki matakai na musamman domin shirin karbar gwamnan, inda ta tanadi lamba ta musamman a gare shi a shirin da take yi na rajistar yanar gizo.

APC ta shirya tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a cikin ofishinsa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook
“Mun fara rajistar yanar gizo, kuma mun tanadi lambar rajista 001 domin gwamnan. Hakika gaskiya ne. Mun tanadi wannan lamba a mazabarsa ta Chiranci-Diso."

- Ibrahim Zakari Sarina

A cewarsa, wannan shiri ba gwamnan kadai ya shafa ba, domin APC a shirye take ta karbi mambobin majalisar zartarwarsa, magoya bayansa da sauran abokan tafiyarsa a siyasa.

NNPP ta yi martani kan ficewar Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi martani kan matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka na yin murabus daga cikinta.

Wanda ya kafa NNPP kuma shugaban kwamitin amintattu na kasa, Bonieface Aniebonam, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bai yi murabus daga jam'iyyar ba.

Bonoface Aniebonam ya bayyana cewa gwamnan na jihar Kano ya fice ne daga tafiyar Kwankwaso wadda Rabiu Musa Kwankwaso yake jagoranta ne ba NNPP ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng