Kwamishinoni 2 Sun Yanke Shawara, Sun Zabi Wanda Za Su Bi tsakanin Abba da Kwankwaso
- Kwamishinoni biyu daga cikin mambobin Majalisar zartarwa ta Kano sun fitar da matsaya kan ficewar Gwamma Abba Kabir Yusuf daga NNPP
- Gwamna Abba dai ya sanar da barin NNPP a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2026 saboda rigingimun cikin gida da suka ki karewa
- Tuni dai yan Majalisar tarayya da na jihar Kano suka fara bin sahun Gwamna Abba, wasu kuma suka ce suna tare da Rabiu Kwankwaso
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mambobin Majalisar zartarwa ta jihar Kano (SEC) sun fara yanke shawara kan bangaren da za su bi tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagora Rabiu Kwankwaso.
Kwamishinan harkokin filaye da tsara birane, Hon Abduljabbar Umar ya bayyana matsayarsa game da ficewar Gwamna Abba daga NNPP.

Source: Facebook
Kwamishina ya bi Gwamna Abba
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Hon. Abduljabbar Umar ya jaddada mubaya'arsa ga Abba, tare da tabbatar da cewa yana tare da mai girma gwamna.
Kwamishinan ya bayyana cewa tun asali, Abba ne ya jawo hannunsa a siyasa, don haka shi ne jagoransa, inda ya bayyana cewa ya fice daga NNPP nan take.
Ya bayyana cewa yana goyon bayan manufofin Abba Gida-Gida na tafiyar da shugabanci mai tsari, tausayin jama'a da mulki bisa gaskiya da rikon amana.
Hon. Abduljabbar Umar ya bar NNPP
A sanarwar da ya fitar, Ho. Abduljabbar ya ce:
"Ina sanar da al’umma baki ɗaya cewa a yunkuri na koyi da bin sahun Maigidana, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na fice daga Jam’iyyar NNPP).
"Tafiyata a siyasar Kano ta samo asali ne daga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda shi ne ya shigar da ni harkar siyasa kuma ya kasance shi ne jagora na.
"Ina goyon bayan manufofinsa na shugabanci mai tsari, tausayin jama’a, da mulki bisa gaskiya, kuma zan ci gaba da tsayawa tare da waɗannan akidu."
A karshe, kwamishinan ya yi addu'ar Allah ya yi riko da hannayen gwamna, kuma Allah Ya ba shi nasara a dukkan al’amuran da ya sanya gaba, Ya maimaita masa wannan kujera da yake kai.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya kara samun goyon baya
Haka zalika jagoran Jam'iyyar NNPP na Ungogo kuma kwamishinan kananan hukumomi da masarautun Kano Hon. Muhammed Tajo Othman ya fita daga jam'yyar NNPP.
Hakan dai na kunshe ne a wani gajeren rahoto da Freedom Radio Nigeria ta fitar bayan Gwamna Abba ya bar NNPP a hukumance.
Hadimin Gwamnan Kano ya yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba Gwamnan Kano shawara ta musamman a kan siyasa.
Sunusi Kwankwaso ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan samun rahotanni masu karfi da ke nuna cewa Gwamna Abba Yusuf ya bar NNPP.
Alhaji Sunusi Kwankwaso ya jaddada biyayyarsa ga jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

