Tsugunne ba Ta Kare ba; An Gano Lam'a a Ficewar Gwamna Abba daga NNPP
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP wadda ya lashe zabe karkashinta a 2023
- Wanda ya kafa NNPP, Boniface Aniebonam ya bayyana cewa kp kadan gwamnan bai yi murabus daga jam'iyyar ba
- Boniface Aniebonam ya kafa hujjojin da ke nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bai yi murabus daga NNPP ba duk kuwa da wasikar da ya rubuta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wanda ya kafa NNPP, Boniface Aniebonam, ya yi magana kan murabus din gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam'iyyar.
Boniface Aniebonam ya ce Gwamna Abba bai yi murabus daga jam’iyyar NNPP ba, sai dai daga tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Aniebonam ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso
NNPP ta yi jayayya kan ficewar Gwamna Abba
Ya fitar da sanarwar ne a matsayin martani cikin gaggawa ga rahotannin da suka bazu a kafafen yada labarai kan ficewar gwamnan daga jam’iyyar.
A cikin sanarwar, Aniebonam ya yi jayayya da cewa wasikar murabus din gwamnan ba a aike ta ga sahihin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na NNPP da Major Agbo ke jagoranta ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Hakazalika ya ce ba a mika ta ga shugaban jam’iyyar na jiha ko sakataren mazaba ba, illa dai ga wani mamba na tafiyar Kwankwasiyya a mazabar Diso-Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
“Kwamitin gudanarwa na kasa na NNPP ba amince da da shugaban Kwankwasiyya a mazabar a matsayin shugaban jam’iyya."
- Boniface Aniebonam
NNPP ba ta san da murabus din Abba ba
Sai dai Aniebonam ya ce a matsayinsa na shugaba, wanda ya kafa jam’iyyar kuma shugaban kwamitin amintattu (BoT) na NNPP, bai da labarin murabus din Gwamna Abba da sauran masu rike da mukaman siyasa na jam’iyyar.
“Jam’iyyar NNPP ta dage dakatarwar da ta yi wa gwamnan daga zama mamba, tare da umartar sa da ya dauki nauyin jagorancin jam’iyyar, kasancewarsa shi ne mafi girman zababben jami’in jam’iyyar.”
"Za ku tuna cewa hukuncin babbar kotun jihar Abia da kuma babbar kotun Abuja, sun umarci INEC da ta amince tare da mika ragamar tafiyar da NNPP ga kwamitin amintattu na jam’iyyar karkashin jagorancin Aniebonam.”
“Har ila yau, babbar kotun Abuja ta bayar da umarnin hana INEC mu’amala ko gudanar da wata harka da tafiyar Kwankwasiyya." “NNPP jam’iyya ce da aka yi wa rijista a hukumance, yayin da tafiyar Kwankwasiyya ke matsayin kungiyar matsin lamba a cikin jam’iyyar."
“Abba Kabir Yusuf da sauran ‘yan majalisar dokoki a jihar Kano sun lashe zabensu ne a karkashin tutar NNPP, tare da tambarin kwandon ‘ya’yan itatuwa, ba tambarin Kwankwasiyya na littafi da launin ja ba.”
- Boniface Aniebonam

Source: Facebook
NNPP ta nuna yatsa ga INEC
Aniebonam ya bayyana jinkirin da INEC ke yi wajen sabunta bayananta da saka sunayen Major Agbo da Oginni Olaposi a matsayin shugabannin NWC a matsayin kura-kurai daga bangaren gudanarwar hukumar.
“Mun lura da dalilan da Abba Kabir Yusuf ya bayar na murabus, amma abin da ya tabbata shi ne NNPP ba ta da wata matsala da gwamnan, haka kuma ba ta tsoma baki a kan duk wani mataki na kashin kansa da ya ga dama ya dauka.”
“Mun dora alhakin halin da mambobin Kano da ke son ficewa kan tsauraran matakan da Kwankwaso ke dauka, wanda abin takaici ne matuka."
- Boniface Aniebonam
Shugabar ALGON ta bi sahun Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabar kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Kano ta yi murabus daga jam'iyyar NNPP.
Hajiya Sa'adatu Salisu Soja ta ce ta yi murabus din ne domin bin sahun gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Ta nuna godiyarta ga shugabanni, mambobi da magoya bayan jam'iyyar NNPP kan hadin kan da suka ba ta lokacin da take jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

