NNPP Na Ci Gaba da Rasa Jiga Jigai, Shugabar ALGON Ta Bi Sahun Gwamna Abba

NNPP Na Ci Gaba da Rasa Jiga Jigai, Shugabar ALGON Ta Bi Sahun Gwamna Abba

  • Shugabar karamar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, Hajiya Sa'adatu Salisu Soja, ta yi murabus daga jam'iyyar NNPP
  • Hajiya Sa'adatu wadda ke shugabantar kungiyar ALGON ta ce tana tare da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Ta zayyano dalilan da suka sanya ta yanke shawarar yin murabus daga jam'iyyar NNPP wadda ta lashe zabe karkashinta a hukumance

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma shugabar kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) a jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta bi sahun Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hajiya Sa'adatu Salisu Soja ta yi murabus daga jam’iyyar NNPP a hukumance a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairun 2026.

Shugabar ALGON a Kano ta fice daga NNPP
Hajiya Sa'adatu Salisu Soja da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sa'adatu Salisu Abdullahi, Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Murabus dinta na kunshe ne cikin wata wasika mai kwanan watan ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, wadda ta sanya a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

2027: APC ta tabo batun b Gwamna Abba tikitin takara kai tsaye bayan barin NNPP

Hajiya Sa'adatu Salisu ta aika da wasikar ga shugabannin jam'iyyar NNPP a karamar hukumar Tudun Wada.

“Ni Hajiya Sa'adatu Salisu Soja ina sanar da murabus dina daga jam’iyyar NNPP daga ranar Juma'a, 23 ga watan Janairun 2026."

-Hajiya Sa'adatu Salisu Soja

Meyasa Sa'adatu Soja ta fice daga NNPP?

Hajiya Sa'adatu Salisu Soja, wadda ita ce kadai zababbiyar shugabar karamar hukuma mace a jihar Kano, ta ce murabus din nata ya samo asali ne daga burinta na bin sahun gwamnan jihar.

"Na yanke shawarar yin murabus ne domin na bi sahun shugabana, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano.”

- Hajiya Sa'adatu Salisu Soja

Ta kara da cewa ta dauki wannan mataki ne bayan yin nazari mai zurfi, domin tallafa wa ajandar cigaban jihar Kano da al’ummarta ta hanyar ayyuka da tsare-tsare masu ma’ana.

“Dangane da wannan dalili, a nan nake sanar da yin murabus dina daga kasancewa mamba a jam’iyyar."

- Hajiya Sa'adatu Salisu Soja

Hajiya Sa'adatu ta yi godiya ga jam'iyyar NNPP

Kara karanta wannan

Daga fitowa gida, 'yan Boko Haram sun harbe malamin addini da jami'an tsaro har lahira

Haka zalika, ta nuna godiyarta ga shugabannin jam’iyyar da mambobinta bisa goyon bayan da suka bata a lokacin da take cikinta.

“Ina godiya ga shugabannin jam’iyyar da mambobinta bisa dukkan goyon bayan da suka nuna mini a lokacin da nake mamba a wannan babbar jam’iyya."

- Hajiya Sa'adatu Salisu Soja

Hajiya Sa'adatu Salisu Soja ta bi sahun Gwamna Abba
Shugabar karamar hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa'adatu Salisu Soja Hoto: Sa'adatu Salisu Abdullahi
Source: Facebook

Gwamna Abba ya rabu da NNPP

A ranar Juma’a da ta gabata, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP a hukumance

Gwamnan ya danganta matakin da ya dauka kan rikice-rikicen cikin gida da ke kara tsananta, da kuma bukatar kare muradun al’ummar jihar Kano.

Rahotanni sun ce gwamnan ya yi murabus ne tare da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano 21, ‘yan majalisar wakilai takwas, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano.

Kwankwaso ya fice daga gwamnatin Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai ba gwamnan Kano shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa.

Sunusi Kwankwaso ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan samun rahotanni masu karfi da ke nuna cewa Gwamna Abba Yusuf ya bar NNPP.

Tsohon Mai ba gwamnan na jihar Kano shawara ya ce tun da farko ya rubuta takardar murabus ya mika, amma ba a karba ta a hukumance ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng