Buba Galadima Ya Fallasa Yadda aka Zuga Abba kan Rabuwa da Kwankwaso

Buba Galadima Ya Fallasa Yadda aka Zuga Abba kan Rabuwa da Kwankwaso

  • Jagoran NNPP, Buba Galadima, ya ce akwai matsin lamba da ake yi wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin ya rabu da Rabiu Musa Kwankwaso tun farkon mulkinsa
  • Ya bayyana haka ne yayin da ake rade-radin fitar Abba Kabir Yusuf daga NNPP kafin gwamnan ya dauki matsaya a hukumance wajen fita daga tafiyar Rabiu Kwankwaso
  • Bugu da kari, ya ce rikicin siyasar Kano ya shafi manyan jam’iyyu, ya zargi APC da gwamnatin tarayya da sa ido kan yadda lamarin zai kasance, musamman kan Kwankwaso

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jagoran jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi bayani dalla-dalla kan rikicin siyasar Kano da ya kunno kai tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Bayanan Buba Galadima sun zo ne 'yan sa'o'i kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da fita daga jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar.

Jagoran NNPP a Najeriya, Buba Galadima
Buba Galadima yana magana a taron siyasa. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi da Trust TV ta wallafa a Facebook, inda aka tambaye shi kai tsaye kan rade-radin cewa ana matsa wa gwamnan lamba ya rabu da Kwankwaso.

An nemi Abba ya rabu da Kwankwaso

Da aka tambayi Buba Galadima ko yana sane da matsin lamba da ake yi wa Abba Kabir Yusuf domin ya watsar da Kwankwaso, sai ya amsa da cewa sun san da hakan tun bayan ayyana Abba a matsayin gwamnan Kano.

Ya ce:

“Ku saurare ni. Bayan an ayyana Abba a gwamnan Kano. Watanni uku kacal bayan hawansa, mun san wadanda ke zuga shi ya bar Kwankwaso.”

Buba Galadima ya kara da cewa ba ya son ya zurfafa cikin batun, yana mai cewa matsin lamba na iya zuwa daga ko’ina, ko daga cikin Kano ko kuma daga Abuja.

Daily Tust ta wallafa cewa ya ce Abba ya dade tare da Kwankwaso tsawon lokaci, kuma watakila yana kokarin rage karfin alakar ne, amma ba shi da tabbaci (domin a lokacin gwamnan bai bar NNPP ba).

Kara karanta wannan

Abba Kabir: Buba Galadima ya yi zazzaga kan maciya amanar Kwankwaso

Tasirin Kwankwaso a siyasar Kano

A cewar Buba Galadima, dukkan zababbun shugabanni a Kano sun san cewa bayan Allah, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya taka rawar gani wajen samar musu da mukamai.

'Dan siyasar ya ce kusan dukkan shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisa sun fito ne daga makarantar siyasar Kwankwaso.

Rabiu Kwankwaso yana magana da 'yan Kwankwasiyya
Sanata Rabiu Kwankwaso yana magana a gidansa na Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya jaddada cewa ba APC kadai ba, har ma da PDP da sauran jam’iyyu a Kano, babu wani zababben dan siyasa da bai taba amfana ta tafarkin Kwankwasiyya ba.

Buba Galadima ya musanta ikirarin cewa NNPP jam’iyya ce mai rikice-rikice da bangarori. Ya ce idan har jam’iyyar ta rabu gida biyu, da ba za ta kasance a tsarin INEC ba.

Buba Galadima ya gargadi Abba Kabir

A wani labarin, kun ji cewa jagoran NNPP, Buba Galadima ya yi magana game da makomar siyasar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Buba Galadima ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sadaukar da dukiyarsa da abubuwa da dama kan nasarar zaben Abba.

A kan haka, Buba Galadima ya ce idan Abba Kabir Yusuf ya ci amanar Rabiu Kwankwaso lallai zai gani a kwaryar tuwonsa a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng