Tsagin Kwankwaso a NNPP Ya Yi Martani Mai Zafi kan Ficewar Gwamna Abba daga Jam'iyya

Tsagin Kwankwaso a NNPP Ya Yi Martani Mai Zafi kan Ficewar Gwamna Abba daga Jam'iyya

  • NNPP ta bayyana bacin ranta da matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka na ficewa daga jam'iyya, inda ta ce hakan cin amana ne
  • Mai magana da yawun NNPP na tsagin Kwankwaso, Ladipo Johnson ya bayyana cewa tarihi ya nuna masu cina amanar siyasa a Kano ba su kai labari
  • Ya roki yan Kwankwasiyya su kwantar da hankulansu, kada su shiga duk wani abu da zai kawo tada zaune tsaye a jihar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jam’iyyar NNPP ta nuna bacin ranta game da ficewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana matakin a matsayin cin amanar talakawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, sakataren yada labarai na tsagin NNPP, Ladipo Johnson, ya ce an zabi Abba ne sakamakon dadewa da ya yi yana fafutuka a tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Abin da aka yi wa tutar NNPP a gidan gwamnatin Kano ya ja hankalin mutane, bidiyo ya fito

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a wajen taron Majalisar zartarwa Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Johnson ya yi watsi da ikirarin gwamnan na cewa ya fice ne saboda rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a cikin jam’iyyar NNPP, kamar yadda The Cable ta ruwaoto.

NNPP ta ce Gwamna ya ci amana

Kakakin jam'iyyar NNPP ya bayyana hujjar da Abba ya bayar ta rikicin cikin gida a matsayin "maras tushe" kuma shure-shure ne kawai.

Johnson ya ce:

“Abin takaici ne da bakin ciki yadda muka samu labarin ficewar Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP.
“Mun yi matukar nadama yadda Gwamna Abba, mutumin da mutanen Kano suka amince wa saboda shekaru da dama na biyayya da sadaukarwa ga tafiyar Kwankwasiyya, yanzu ya zabi ya ci amanar talakawa."

NNPP ta tuna abin da ya faru da Rimi

Sakataren yada labaran ya kamanta wannan lamarin da abin da ya faru a siyasar Kano a farkon shekarun 1980, lokacin da tsohon gwamna, Abubakar Rimi, ya fice daga jam’iyyar PRP zuwa NPP

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Gwamna Abba na Kano ya fice daga jam'iyyar NNPP

Ya tuna cewa duk da sauya shekarar Rimi tare da mafi yawan zababbun jami’an Kano a wancan lokacin, masu kada kuri’a suka juya masu baya a 1983, wanda hakan ya sa suka sha kaye a zabe.

Ya kara da cewa mutum daya ne kacal ya samu nasara daga cikin mambobin majalisar dokokin jihar da suka sauya sheka tare da Rimi.

Jagoran NNPP.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: KwankwasoRM
Source: Facebook

Sakon NNPP da jama'ar Kano

Yayin da yake bayyana tafiyar Abba a matsayin abu mai raɗaɗi, kakakin na NNPP ya bukaci mazauna jihar Kano da magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu, su kuma guji ayyukan da za su tada tarzoma.

Johnson ya tunatar da cewa tarihi ya nuna cewa masu kada kuri’a sukan hukunta rashin biyayya da butulci a siyasa, kamar yadda Punch ta kawo.

Yan Majalisa 2 sun sahun Gwamna Abba

A wani labarin, mun kawo cewa yan Majalisar tarayya biyu daga Kano sun yanke shawarar bin Abba Gida-Gida, sun mika takardar murabus daga jam'iyyar NNPP a hukumance.

'Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kumbotso a majalisar wakilai, Hon. Dankawu Idris ya fice daga jam'iyyar NNPP domin bin Abba sau da kafa.

Haka zailka, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, mamba mai wakiltar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado a Majalisar wakilai ya mika takardar ficewarsa daga NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262