Abin da Aka Yi Wa Tutar NNPP a Gidan Gwamnatin Kano Ya Ja Hankalin Mutane, Bidiyo Ya Fito

Abin da Aka Yi Wa Tutar NNPP a Gidan Gwamnatin Kano Ya Ja Hankalin Mutane, Bidiyo Ya Fito

  • An cire tutar NNPP daga fadar gwamnatin jihar Kano bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar
  • Wannan ci gaba na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja
  • Bidiyon cire tutar ya ja hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu suka bayyana lamarin da halin 'yan siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - A yau Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2025, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ta sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a hukumance

Gwamna Abba ya tabbatar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban NNPP na mazabar Diso-Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wani taro a gidan gwamnatinsa Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Faceook yau Juma'a.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisar tarayya 2 daga Kano sun bi sahun Gwamna Abba, sun fice daga NNPP

An cire tutar NNPP a gidan gwamnatin Kano

Sai dai jim kadan bayan wannan sanarwa, wani faifan bidiyo ya fara yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga wani jami'i ya fitar da tutar NNPP daga fadar gwamnatin Kano

Faifan bidiyon ya nuna yadda mutumin ya nannade tutar NNPP, sannan ya dauke ta ya yi waje da ita a gidan gwamnatin da ke cikin birnin Kano, lamarin da ya kara tabbatar da ficewar Abba Gida-Gida.

Har yanzu dai ba a ji ta bakin jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Injiniya Rabiu iMusa Kwankwaso kan wannan mataki da Abba ya dauka ba.

Sai dai ana tsammanin Gwamna Abba zai sanar da komawa jam'iyyar APC a hukumance nan ba da jimawa ba.

Wani mai amfani da shafin X, Imran Muhammad ya wallafa faifan bidiyon lokacin da aka cire tutar NNPP daga gidan gwamnatin Kano.

Martanin mutane kan cire tutar NNPP

Bayan wannan bidiyo ya fara yawo, 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan cire tutar NNPP da kuma ficewar Gwamna Abba daga jam'iyyar. Mun tattaro muku wasu daga ciki:

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Gwamna Abba na Kano ya fice daga jam'iyyar NNPP

Hephziba Behulah ya ce:

"Za ka yi nadama, su 'yan siyasa ba su da kunya, 'yan Najeriya kuma ba su da kwalwalwar rike abu, amma duk da haka ku rubuta wannan ku ajiye."

Maryam Cissey ta ce:

"Lokacin da na gaya muku gwamnan jihar Kano bai san abin da yake yi ba, zagi na kuka yi. Ku gan shi yanzu bayan ya kasa kawo wani babba abin ci gaba a jihar Kano.

Hamman Atiku ya ce:

"Ku lura da kyau, shi kan sa wanda ya cire tutar NNPP, ba jar hula ba ce a kansa."
Gwamna Abba.
Wani jami'i ya dauke tutar NNPP daga fadar gwamnatin Kano bayan Abba Kabir Yusuf ya bar jam'iyyar Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba zai tura tawaga ga Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai kafa kwamitin jakadu don sanar da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso sauyin sheƙarsa zuwa APC.

Wata majiya mai tushe da ta halarci wata ganawar sirri da aka gudanar da daddare ta shaida wa manema labarai matsayar da aka cimma game da batun sauya sheka.

Majiyar ta ce Gwamnan ya amince cewa, bisa ladabi da girmamawa, ya dace a sanar da Kwankwaso a hukumance kafin a bayyana sauyin sheƙar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262