Babbar Magana: Atiku Ya ‘Tono’ Shirin Majalisa na Taya Tinubu Magudin Zabe
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi Majalisar Tarayya da shirin magudin zaben 2027
- Atiku ya ce gibin da ke cikin Dokar Zabe ta 2022 ne ya haddasa rikice-rikicen zaben 2023 tare da wahalar kalubalantar sakamako
- Ya gargadi Majalisar Dattawa cewa rashin gyara dokar kafin 2027 na iya zama shiri tun da wuri na lalata sahihancin zaben gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi Majalisar Tarayya da shirya magudin zaben 2027.
Atiku ya ce Majalisar Dattawa ta shimfida hanya domin magudin babban zaben shekarar 2027 ta hanyar jinkirta gyaran Dokar Zabe ta 2022.

Source: Facebook
Atiku ya fara babatu kan zaben 2027
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (da aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis 22 ga watan Janairun 2026.
Ya ce gibin da ke cikin dokar zaben da ake amfani da ita yanzu ya taka rawa sosai wajen matsalolin da suka biyo bayan zaben 2023.
Ya ce irin wannan gibi ne suka ba da damar tafka magudi a zabe tare da hana ’yan takara damar samun nasara wajen kalubalantar sakamakon zabe a kotu.
Atiku ya rubuta cewa:
“Babban koma-baya da aka fuskanta a zaben 2023 shi ne gibin da ke cikin Dokar Zabe ta 2022, wanda ya ba da dama ga yawaitar magudi tare da kusan hana masu shigar da kara samun nasara a kotu.”
A cewarsa, idan ana son gyara kura-kuran da aka gani a zaben 2023, dole ne a gaggauta sake duba tsarin doka da ke tafiyar da zabe kafin a kai ga shekarar 2027.
Sai dai ya zargi Majalisar Dattawa da nuna halin ko-in-kula wajen amincewa da gyare-gyaren da ake bukata a dokar.

Source: Facebook
Atiku ya kawo hujja game da zarginsa
Atiku ya ambaci wani rahoto na 'Foundation for Investigative Journalism' (FIJ), inda ya bayyana rahoton a matsayin hujja da ke nuna gazawar Majalisar Dattawa tare da tunasar da ita nauyin da ke kanta na yi wa jama’a adalci.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya fara bambami tun yanzu, ya soki Sanatoci kan taba dokar zabe a majalisa
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce sahihancin zaben 2027 zai dogara ne da yadda Majalisar Dattawa za ta dauki wannan kudiri da muhimmanci cikin gaggawa.
Ya kara da cewa duk wata gazawa wajen gyara dokar kafin zaben 2027 na nufin shiri ne na ganganci domin lalata tsarin zabe tun kafin a kada kuri’a.
A karshe, Atiku ya jaddada cewa:
“Duk abin da bai tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2027 karkashin sabuwar dokar da aka gyara ba, to yunƙuri ne na magudin zabe tun kafin jama’a su je rumfunan kada kuri’a.”
An fadi wanda ya cancanta da tikitin ADC
Kun ji cewa tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana game da abin da zai yi saurin ruguza ADC.
Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar ADC za ta shiga rikici idan Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Tsohon hadimin shugaban kasan ya ce Atiku na da karfin samun tikitin ADC, amma hakan zai sa ‘yan takara da magoya baya da dama su fice.
Asali: Legit.ng
