Kano: Abba Ya Tashi Tawaga, Zai Sanar da Kwankwaso Shirinsa na Koma wa APC
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai kafa kwamitin jakadu don sanar da Rabiu Kwankwaso sauyin sheƙarsa zuwa APC
- ‘Yan Majalisar Tarayya da na Jiha da dama na cikin shirin sauyin sheƙar daga jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano zuwa APC
- Gwamnan zai sanar da murabus dinsa bayan an kammala ganawa da jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata tawaga ta musamman domin sanar da jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, game da shirin sauyin sheka zuwa APC.
Wata majiya mai tushe da ta halarci wata ganawar sirri da aka gudanar da daddare ranar Alhamis ta shaida wa manema labarai matsayar da aka cimma game da batun sauya sheka.

Source: Twitter
Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin gwamnan da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano.
APC: An tattauna sauya shekar Abba
Majiyar ta ce Gwamnan ya amince cewa, bisa ladabi da girmamawa, ya dace a sanar da Kwankwaso a hukumance kafin a bayyana sauyin sheƙar.
A cewar bayanan da suka fito daga ganawar, ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun bukaci Gwamnan da ya je da kansa ya gana da Kwankwaso.

Source: Twitter
'Yan majalisar sun bayyana cewa hakan zai nuna girmamawa da kuma mutunta rawar da Kwankwaso ya taka a siyasar gwamnan.
Sai dai gwamnan, a cewar majiyoyin, ya ki amincewa da zuwa da kansa, inda ya ce Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibrin Falgore, ne ya dace ya jagoranci tawagar jakadun a madadinsa.
An turje kan maganar AP da Kwankwaso
Majiyoyi sun kara da cewa Rt. Hon. Jibrin Falgore, ya nuna rashin jin dadinsa da wannan umarni, inda ya bayyana cikin ladabi cewa ba zai iya fuskantar Rabiu Kwankwaso da irin wannan batu mai nauyi ba.
Duk da haka, Gwamnan na sa ran kafa kwamitin da zai kunshi ‘yan Majalisar Tarayya da ta Jiha, tare da wasu 'yan majalisar zartarwarsa, domin su kai ziyara ga Kwankwaso a ranar Juma’a.
Tawagar za ta isar da sakon gwamnan a hukumance tare da bayyana dalilan sauyin sheƙar da kuma matakin da ake shirin dauka nan gaba.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran gwamnan zai bayyana murabus dinsa daga NNPP kwana guda bayan da tawagar ta kammala sanar da Rabiu Kwankwaso.
Gwamna Abba zai bar NNPP a karshen mako
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tsayar da wata rana ta daban domin sauya sheka daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan jerin dage wa da jinkirin da aka yi fama da su kan batun sauyin jam’iyyar gwamnan.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnan ya sanar da wannan rana ne bayan wani taron sirri da aka gudanar da tsakar dare na ranar Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

