Kasuwar Teloli da Ƴan Yadi Ta Bude Suna Caɓawa ana Shirin Karbar Abba a APC

Kasuwar Teloli da Ƴan Yadi Ta Bude Suna Caɓawa ana Shirin Karbar Abba a APC

  • Teloli da ’yan kasuwar yadudduka a Kano na samun cunkoson aiki bayan karuwar bukatar kayan APC ana jita-jitar sauya jam’iyyar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • A wasu manyan kasuwannin Kano, ana sayen yadudduka da huluna masu launin fari, kore da ja masu alamar APC yayin da masu dinki ke aiki dare da rana
  • Ana ta rade-radin cewa yau ko gobe Abba Kabir Yusuf wanda ya ci zabe a karkashin tsarin Kwankwasiyya da jam'iyyar NNPP zai koma APC mai-ci a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Teloli da ’yan kasuwar yadudduka a jihar Kano sun bayyana yadda suke ciniki a yan kwanakin nan.

'Yan kasuwar suka ce suna samun karuwar aiki sakamakon jita-jitar sauya sheka da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke shirin yi.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda ake kyamatar yan uwan Fatima da aka yi wa kisan gilla a zaman makoki

Yadda kasuwar teloli ta bude ana shirin karbar Abba a APC
Gwamna Abba Kabir da teloli a bakin aiki. Hoto: MICHELE SPATARI / Contributor, PIUS UTOMI EKPEI / Stringer, X/Kyusufabba (An yi amfani da hotunan ne domin misali kawai).
Source: Getty Images

Kasuwa ta budewa teloli, masu yadi a Kano

Rahoton Legit.ng ya nuna cewa bukatar kayan APC ta karu matuka, musamman yadudduka da huluna masu launin fari, kore da ja.

A manyan kasuwanni irin su Kantin Kwari da Fagge, masu dinki da masu hula na aiki ba tare da hutawa ba domin biyan bukatar kwastomomi.

Majiyoyi sun ce bukatar ta karu ne cikin makonni biyu da suka gabata, yayin da magoya baya da jami’an gwamnati ke shirin shiga sabuwar siyasa.

Wani mai dinki a Gadon Kaya, Mallam Hassan, ya ce bai taba ganin irin wannan cunkoso na aiki ba ko a lokacin zabe.

Ya ce mutane na kawo yadudduka suna yin oda har guda biyar zuwa 10 lokaci guda, lamarin da ya sa suke aiki dare da rana.

“Wannan abin ba a saba gani ba ne. Tun bayan da jita-jitun cewa Gwamnanmu zai koma APC suka karu, abokan huldata suna kawo zaren “shadda” fari da yadi don a dinka a cikin launuka kore, fari da ja.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

"Wasu suna kawo odar saiti biyar zuwa 10 a lokaci guda. Muna dinki dare da rana."

- Malam Hassan

Ana ci gaba da shirye-shiryen karbar Abba Kabir a APC
Gwamna Abba Kabir yayin zaman majalisar zartarwa a Abuja. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Mazauna Kano sun magantu game da kasuwa

Shi ma Alhaji Abubakar, mai sayar da hula a Kwari, ya ce sayar da hulunan APC ya ninka sau uku cikin kankanin lokaci.

Ya ce mutane na son su shirya tun wuri domin ka da a bar su a baya idan aka fara gangamin siyasa.

Wani dillalin yadi, Alhaji Ahmed Bello, ya ce farin yadi na fita fiye da sauran launuka saboda alamar biyayya ta siyasa.

Masana siyasa sun bayyana cewa a Kano, sutura na nuna bangare da biyayya, musamman a lokacin sauyin siyasa.

Sun ce ko da sanarwar sauya jam’iyya ta makara, tattalin arzikin ’yan kasuwa ya riga ya amfana, abin da ya zama riba ga masu sana’a.

Tanadin da APC ta yi wa Abba Kabir

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Kano ta bayyana shirin da ta yi game da fara rijistar mambobinta da ake yi a kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Sarki Sanusi II ya roki Abba ya yi ga makasa Fatima da 'ya'yanta 6

APC ta bayyana cewa ta tanadi katin mambobinta mai lamba 001 domin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yayin fara rijistar yana gizo a jihar.

Kakakin APC, Ahmad Aruwa, ya ce an jinkirta fara rajistar ne domin bai wa gwamnan damar shigowa jam’iyyar cikin tsari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.