Kano: Abin da APC Ta Yi wa Abba kan Rijistar Zama Dan Jam'iyya kafin Sauya Sheka

Kano: Abin da APC Ta Yi wa Abba kan Rijistar Zama Dan Jam'iyya kafin Sauya Sheka

  • Jam’iyyar APC a Kano ta bayyana shirin da ta yi game da fara rijistar mambobinta yayin da ake jiran shigowar Gwamna Abba Kabir
  • APC ta bayyana cewa ta tanadi katin mambobinta mai lamba 001 domin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yayin fara rijistar yana gizo a jihar
  • Kakakin APC, Ahmad Aruwa, ya ce an jinkirta fara rajistar ne domin bai wa gwamnan damar shigowa jam’iyyar cikin tsari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi karin haske game da fara rijistar katin jam'iyya da aka fara yi a fadin kasa baki daya.

Jam'iyyar ta tabbatar da cewa ta tanadi katin mambobinta mai lamba 001 domin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

APC ta fara rijistar kati yayin ake jiran Abba Kabir
Shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Abdullahi Abbas, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

APC ta ware kati na musamman domin Abba

Kakakin jam’iyyar APC a Kano, Ahmad Aruwa, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis 22 ga watan Janairun 2026, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta gaji da jiran Abba ya sauya sheka, an fara yi wa jama'a rajista

Ya ce matakin na zuwa ne bisa tsammanin sauya sheƙar gwamnan daga jam’iyyarsa zuwa APC nan ba da jimawa ba.

A cewarsa, jam’iyyar ta jinkirta fara aikin rijistar ne da gangan, domin bai wa gwamnan damar shiga jam’iyyar cikin tsari mai kyau.

Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta fara rajistar mambobi ta yanar gizo (e-registration) a fadin jihar.

Ahmad Aruwa ya ce an kaddamar da rajistar yanar gizo a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda ya bukaci duk masu sha’awar shiga jam’iyyar su je mazabunsu domin yin rajista.

Ya ce:

“Muna kuma sa ran gwamnan zai shigo jam’iyyar nan ba da jimawa ba, kuma mun riga mun tanada masa katin memba mai lamba 001 a mazabarsa.”
APC ta tanadi kati na musamman ga Abba abir yayin rijista
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Dalilin kafa kwamiti da APC ta yi

A wani bangare na shirye-shiryen gudanar da rajistar, jam’iyyar ta kafa kwamitin mutum 14 da zai kula da aiwatar da aikin e-rijistar a fadin jihar Kano.

Tun da fari, shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Abba Kabir Yusuf zai yi rajista tare da karbar katin mambobinsa tsakanin ranar Talata zuwa Laraba mai zuwa.

Kara karanta wannan

'APC za ta fadi a 2027,' An aika wa Tinubu sakon shan kaye a zabe mai zuwa

Abbas ya ce hakan na iya faruwa ne bayan dawowar gwamnan daga Abuja, inda ya halarci wata ganawa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban APC din ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kimanin ma’aikatan wucin gadi 1,500 da aka dauka domin gudanar da rajistar.

APC ta fara rijistar mambobinta a Kano

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta fara rijistar mambobinta ta yanar gizo bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke jan kafa wajen sauya sheka.

An ce a baya sun bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a dage fara rajista har sai Gwamna ya koma APC.

Sai dai da alama ana samun jan kafa, domin kawo yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf bai sanar da sauya sheka ko sa ranar da zai koma APC ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.