Lissafi Ya Canza, Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnan PDP a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
- Wannan ganawa na zuwa ne makonni kadan bayan gwamnan Filato, Barista Caleb Mutfwang ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Gwamna Makinde na daya daga cikin tawagar G-5, wacce ta yi wa Bola Tinubu aiki a zaben shugaban kasa na shekarar 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kai ziyara fadar shugaban kasa da birnin tarayya Abuja yau Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa daga zuwan Gwamna Makinse, ya wuce kai tsaye ya shiga ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan ganawa ta sake haifar da sabon hasashe na siyasa a daidai lokacin da ake ci gaba da sauya sheƙa kafin zaɓen 2027.
Ganawar Tinubu da Gwamna Makinde, wanda yana daya daga cikin manyan jagororin jam’iyyar adawa ta PDP, na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya koma APC.
Gwamnan Oyo na daga cikin gwamnonin PDP guda biyar da aka fi sani da G-5, waɗanda suka yi adawa da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.
Sauran mambobin G-5 sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma Ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike; tsohon Gwamnan Benue, Samuel Ortom; tsohon Gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi; da tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.
Sai dai daga baya, Gwamna Makinde da Wike sun samu saɓani a tsakaninsu, lamarin da ya jawo suka rika musayar yawu musamman kan rigingimun da suka addabi PDP.
A wata hira da ya yi kwanan nan, Makinde ya ce rikicin ya samo asali ne daga wata ganawa da suka yi da Tinubu, inda Wike ya yi alƙawarin dukusar da PDP domin shugaban kasa ya yi tazarce a 2027.
“Mun yi wani taro da Shugaban Ƙasa tare da Wike da wasu mutane, sai Wike ya ce wa Shugaban Ƙasa zai rike masa PDP don ya samu sauki a 2027. Sai muka tashi, na tambaye shi, shin mun amince da wannan?” in ji Makinde.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng

