Shirin Tsige Gwamna Fubara Ya Gamu da Cikas, Babban Alkali Ya Aika Wasika ga Majalisa

Shirin Tsige Gwamna Fubara Ya Gamu da Cikas, Babban Alkali Ya Aika Wasika ga Majalisa

  • Babban alkalin jihar Rivers ya yi biyayya ga umarnin kotu game da dambarwar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisa
  • Mai shari’a Simeon Amadi ya aika wa Majalisar dokoki cewa ba zai kafa kwamitin bincike kamar yadda ta bukata ba saboda umarnin kotu
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisar ta umarci babban alkalin ya kafa kwamitin da zai bincike laifuffukan da ake zargin Fubara da mataimakiyarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigera - Babban Alkalin Jihar Rivers, Mai shari’a Simeon Amadi, ya kawo tangarda a shirin Majalisar dokoki na tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.

Babban alkalin ya ƙi amincewa da buƙatar Majalisa na kafa kwamiti domin binciken Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuffuka.

Gwamnan jihar Rivers.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara a gidan gwamnati da ke Fatakwal Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Umarnin da Majalisa ta ba babban alkali

Kara karanta wannan

Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar Dokokin Jihar Rivers, a kwanakin baya, ta zartar da kuduri tare da umartar Babban Alkalin da ya kafa kwamitin mutane bakwai domin binciken zarge-zargen da ake yi wa gwamnan da mataimakiyarsa.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a matsayin wani bangare na yunkurin tsige su daga mulki.

Babban alkalin Rivers ya dauki matsaya

Sai dai a cikin wata wasika mai kwanan watan 20 ga Janairu, 2026, wadda ya aike wa Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule, Mai shari’a Amadi ya ce doka ta hana shi daukar irin wannan mataki, saboda akwai umarnin kotu.

Babban Alkalin ya bayyana cewa ofishinsa ya karɓi umarnin kotu guda biyu na wucin-gadi a ranar 16 ga Janairu, 2026, bayan da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa suka shigar da ƙara.

A cewarsa, umarnin kotun guda biyu sun hana shi karɓa, dubawa ko aiwatar da duk wata bukata, kuduri ko takarda da ta shafi tsige gwamnan da mataimakiyarsa daga mulki.

Majalisar Rivers ta daukaka kara

Mai shari’a Amadi ya kuma bayyana cewa Kakakin Majalisar ya riga ya kalubalanci umarnin a Kotun Daukaka Kara da ke Fatakwal, kuma an mika wa ofishinsa takardun daukaka kara a ranakun 19 da 20 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji

Ya ce bisa ka’idar shari’a, dole ne dukkan bangarori su jira hukuncin Kotun Daukaka Kara kafin daukar wani mataki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

“Saboda wadannan umarnin kotu da kuma daukaka karar da aka shigar, a yanzu hannuna a daure yake, ba zan iya yin komai ba.
"A halin yanzu doka ta hana ni aiwatar da nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mini a sashe na 188(5) dangane da wannan lamari,” in ji shi.
Kakakin Majalisar Rivers.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Rivers, Rt. Hon. Martin Amaewhule yana jagorantar zama a Fatakwal Hoto: Rivers House of Assembly
Source: Facebook

Babban Alkalin ya bukaci ‘yan majalisar da su fahimci halin da ake ciki, tare da roƙon su da su nuna hakuri da fahimta kan matsayarsa game da tanadin doka.

Abin da ya hana Gwamna Fubara magana

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin gwamnan Rivers ya bayyana cewa har yanzu Majalisa ba ta sanar da Gwamna Fubara shirinta na tsige shi a hukumance ba.

Mai ba Gwamnan Rivers shawara kan harkokin siyasa, Darlington Orji, ya ce hakan ne ya sa har yanzu Gwamna Fubara bai fito ya maida martani a hukumance ba.

Ya kara da cewa majalisar ba ta bi ka’idojin doka da kundin tsarin mulki suka tanada ba wajen fara shirin tsige gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262