2027: Alamu Sun Nuna Wasu Ministoci da Hadimai Za Su Rasa Mukamansu a Gwamnatin APC

2027: Alamu Sun Nuna Wasu Ministoci da Hadimai Za Su Rasa Mukamansu a Gwamnatin APC

  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce 'yan jam'iyya da suka mata wahala kadai za a ba mukamai bayan zaben 2027
  • Farfesa Nentawe ya ce zai tsaya tsayin daka wajen tabbatar da 'yan APC ne suka shiga gwamnati, ba wai kwararru ko masu gogewar aiki ba
  • Wannan kalamai na shugaban APC sun fara jan hankali a kafafen sada zumunta, inda wasu ke fargabar hakan zai nakasa shugabanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Alamu sun fara nuna cewa Shuba Bola Ahmed Tinubu ba zai ci gaba da aiki da wasu ministoci da hadiminsa ba bayan ya samu nasara a karo na biyu a zaben 2027.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa bayan zaben 2027, mukaman siyasa za su kasance kacokan ga mambobin jam’iyya APC ne kawai, ba masu kwarewa ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sanya Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC kafin zaben 2027'

Shugaban APC na kasa.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda yayin hira da manema labarai a hedkwatar jam'iyya a Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Daily Trust ta ce Nentawe ta fadi haka ne yayin da yake magana a daren Talata a Abuja a wurin wani taro mai taken “Renewed Hope Promise Kept 2027: Meet and Greet North-West Mobilisation."

Karamin Ministan Ayyuka, Bello Goronyo ya ne ya shirya taron wanda ya maida hankali kan alkawurran da Shugaba Tinubu ya dauka kuma ya cika a Arewa maso Yamma.

Shugaban APC ya tada kura

Farfesa Nentawe ya jaddada cewa shugabanci abu ne na siyasa, don haka dole ne wadanda aka nada su goyi bayan jam’iyyar da ta kawo su kan mulki.

Faifan bidiyon kalamansa ya bazu a kafafen sada zumunta tare da haifar da mahawara mai zafi tsakanin masu sharhin siyasa, mambobin jam’iyya, da kungiyoyin farar hula a fadin kasar.

Martanin sun kasance daban-daban; wasu mambobin jam'iyyar APC sun goyi bayan hakan, yayin da wasu masana ke tsoron hakan zai nakasa shugabanci na gari da ya dogara da ilimi da kwarewa.

Kara karanta wannan

APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba

APC za ta canza tsarin nada mukamai a 2027

A cewar Nentawe, duk wadanda aka nada a gwamnati dole ne su kasance masu fafutukar siyasa a matakin mazabu kuma su dinga shiga harkokin jam’iyya gadan-gadan.

“Ya kamata a ko da yaushe mu dinga waiwaye mu tuna abin da ya kawo mu nan. Kuri’u ne. Da zarar an ba ka mukamin siyasa, kai dan siyasa ne. Shi ke nan,” in ji shi.
Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a wasu takardu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya dage kan cewa zai kare matsayar nan ta cewa mutanen da suke shirye su yi wa APC aiki ne kawai za a duba domin ba su mukamai, kamar yadda The Nation ta rahoto.

“A matsayina na shugaban jam’iyya, zan tsaya tsayin daka wajen kare cewa idan ba ka shirya shiga cikinmu ba, kada a ba ka mukami. Idan kai kana da kwarewar aiki ne to je ka zama mai ba da shawara," in ji shi.

Nentawe ya kara da cewa manufofin gwamnati su ne alkawuran da ta yi a lokacin kamfe, kuma ya zama dole wadanda za su jagoranci aiwatar da su, su kare su, su bayyana su, kuma su tallata su.

Kara karanta wannan

APC ta fayyace wanda zai zama jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

An hango faduwar Tinubu a 2027

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mai neman shugaban kasa a PDP, Gbenga Olawepo-Hashim ya ce babu abin da zai ceci Shugaba Bola Tinubu daga faduwa a zaben 2027.

Olawepo-Hashim ya ce ’yan Najeriya za su yi amfani da kuri’arsu wajen canza gwamnati cikin lumana da bin doka da oda.

Ya zargi jam’iyya mai mulki da kawo matakan da ke nufin raunana 'yan adawa, yana nuna kwarin gwiwar cewa hakan ba zai rushe tsarin dimokuradiyyar kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262