Zance Ya Kare: NNPP Ta Cimma Matsaya kan Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC

Zance Ya Kare: NNPP Ta Cimma Matsaya kan Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC

  • Tsagin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya yi tsokaci kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Shugaban tsagin na NNPP ya bayyana cewa har yanzu Gwamna Abba cikakken mamba ne a jam'iyyar kuma suna mutunta shi
  • Ya bayyana cewa Gwamna Abba yana da 'yancin da zai iya ficewa daga jam'iyyar idan ya ga dama, inda ya bayyana abin da ya kamata ya yi

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsagin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Shugaban tsagin na NNPP, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ya bukaci Gwamna Abba ya rubuta takardar murabus a hukumance ga jam’iyyar NNPP da doka ta amince da ita kafin ya koma APC.

Kara karanta wannan

APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba

NNPP ta yarda Gwamna Abba ya koma APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kano a ranar Talata, 20 ga watan Janairun 2026.

A cewar El-Jibril, kotu ta yanke hukunci a bara cewa bangaren NNPP da ke amfani da tambarin wando mai kayan marmari, wanda ya ke jagoranta a Kano, shi ne sahihin NNPP a Najeriya.

Gwamna Abba na cikin NNPP

Mas'ud El-Jbril Doguwaya nuna wa ‘yan jarida hukuncin kotuna daban-daban, yana mai jaddada cewa bangarensa ne halastaccen NNPP, kuma Gwamna Abba Yusuf har yanzu cikakken mamba ne na jam’iyyar, jaridar Thisday ta kawo labarin.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf har yanzu cikakken mamba ne na NNPP mai tambarin kwando da kayan marmari."
"Abu na biyu, muna kira ga INEC da ta mutunta dukkan hukuncin kotunan da aka yanke a bara kan wannan batu."
"A karshe, ina so in jaddada cewa Abba Kabir Yusuf har yanzu mamba ne na NNPP kuma muna girmama shi.”

Kara karanta wannan

APC ta fayyace wanda zai zama jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

- Sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa

Me NNPP ta ce kan sauya shekar Gwamna Abba?

Mas'ud El-Jibril ya kara da cewa, idan Gwamna Abba yana da niyyar barin jam’iyyar, yana da ’yancin yin hakan a doka, amma dole ne ya gabatar da murabus dinsa a rubuce ga jam’iyyar.
“Har yanzu ba mu karbi wata takardar murabus daga gare shi ba. Zama mamba a jam’iyya abu ne na zabi. Idan ya yanke shawarar barin jam’iyyar, hakkinsa ne, amma dole ne ya bi dokoki da ka’idojin jam’iyyar."

- Sanata Muazu Eljibril

Gwamna Abba na shirin sauya sheka zuwa APC
Gwamnan Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Tsagin na NNPP ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta mutunta hukuncin kotuna, yana mai gargadin cewa:

“Rashin bin wannan umarni zai iya haifar da matsalolin shari’a nan gaba, musamman idan Kotun Koli ta tabbatar da sahihancin wannan bangare.”

APC ta fadi jagora tsakanin Abba da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana wanda zai zama jagoranta a jihar Kano idan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa cikinta.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NNPP ta hango makomarta a Kano bayan ficewar Gwamna Abba

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abadullahi Abbas, ya bayyana cewa maganar waye zai zama jagoran APC bayan mai girma gwamna ya sauya sheka ba abin damuwa ba ne.

Abdullahi Abbas ya ce Gwamma Abba zai rike matsayinsa na jagoran APC a Kano, yayin da Abdullahi Umar Ganduje zai zama uban jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng