‘Gwamna Abba Zai Iya Samun Damar Zama Shugaban Kasa idan Ya Rabu da Kwankwaso’
- Wani 'dan siyasa a Kano ya bayyana damuwa game da dambarwar siyasar jihar inda ya ce abin tausayi ne da takaici
- Aminu Lawal Sufi ya ce rabuwa da Rabiu Kwankwaso alheri ne ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf domin ci gabansa
- Sufi yana zargin Kwankwaso da hana shi gudanar da aiki ga al'umma yadda ya kamata, ya ba shi shawarar komawa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani dan siyasa a jihar Kano ya bayyana alherin da Gwamna Abba Kabir zai iya samu bayan rabuwa da Rabiu Kwankwaso.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar 'Arewa Enlightenment', Aminu Lawal Sufi ya ce rabuwa da Kwankwaso alheri ne ga gwamnan.

Source: Facebook
An shawarci Abba da ya bar Kwankwaso
'Dan siyasar ya bayyana haka ne a wani bidiyo yayin hira da DCL Hausa wanda aka wallafa a shafin Facebook a yau Laraba 21 ga watan Janairun 2026.
Sufi ya bayyana damuwa kan abin ke faruwa a Kano inda ya ce abin tausayi ne da kuma takaici yadda ake juya Abba Kabir.
Ya ce:
"Duk mutumin da ya ke karantar siyasa ya sani cewa abin da tsohon gwamnan Kano yake yi a siyasar jihar sai dai ka ce Innalillahi wa inna ilaihir raji'una.
"Idan ka kalli yadda ya hana gwamnan aiki, ya shiga gwamnati ya hana dukkan wasu abubuwa saboda haka wannan ba daidai ba ne.
"Gwamna Abba ya sani shi aka zaba a matsayin gwamnan Kano, ba Rabiu Kwankwaso ba, soyayyar da ke tsakaninsu kamar ta dan mutum ne da aljani, kullum kona ka yake yi amma yana nuna yana sonka."

Source: Facebook
'Mafita ga Abba Kabir game da Kwankwaso'
Sufi ya ce mafita daya ce ga Abba Kabir shi ne ya bar jikin Kwankwaso zuwa APC idan yana son ci gaba da aiki ga al'umma.
Ya ce zai iya samun kowane irin matsayi idan har ya koma APC saboda damarmaki da ke ciki wanda zai kai shi har ga zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan
APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba
"Babu wata mafita ga gwamnan Kano idan bai rabu da Kwankwaso ba, idan yana son aiki ga jama'a to sai ya ja baya, ba cewa muka yi a bata ba.
"Idan Abba yana son yiwa mutane aiki sai ya ja layi, idan zaka ban shawara kan ban shawara idan babu ka kyale ni saboda ni ke da mafita a wurin Allah.
"Muna son gwamna ya natsu ya zama babban dan siyasa, dawowarsa APC abu na farko zai iya zama daga karamin dan siyasa zuwa babba.
"Na biyu kamar ya fito daga karamin rafi zuwa babban rafi, Allah ne kadai ya san inda siyasarsa za ta tsaya, zai iya zama shugaban kasa ko mataimaki ko minista, haka Kwankwaso ya bi ya zama abin da ya zama a Najeriya."
- Cewar Sufi
'Dan siyasar ya ce babu wanda yake ba da mulki sai Allah, Rabiu Kwankwaso ba zai iya ba wani kujerar madafun iko ba.
'Dan siyasa ya soki tsarin Kwankwaso a Kano
A wani labarin tsohon dan takarar gwamna a Kano, Ja’afar Sani Bello ya yi magana game da dambarwar siyasa da ke faruwa a jihar.
'Dan siyasar ya ce tasirin siyasar Rabiu Kwankwaso ya ta’allaka ne kawai a Kano, yana mai cewa ba shi da karfin tasiri a matakin kasa.
Tsohon mai nema zaman gwamnan ya kuma jero manyan 'yan siyasa a Arewacin Najeriya da suke da tasiri a siyasar yankin gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

