'Yadda Alakar Abba da Kwankwaso Take bayan Jita Jitar Zai Bar NNPP zuwa APC'
- Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya yi magana kan rade-radin dambarwar siyasa tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
- Sanusi Dawakin Tofa ya yi tsokaci kan lamarin siyasar jihar yana mai cewa babu wata matsala tsakanin Gwamna Abba da jagoran Kwankwasiyya
- Mai magana da yawun gwamnan ya jaddada cewa siyasa ba za ta lalata dangantakarsu ba, sai dai duk wani hukunci na gaba da bangarorin biyu suka dauka daga baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mai magana da yawun Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan dambarwar siyasar jihar Kano.
Sanusi Bature D-Tofa ya yi tsokaci ne game alakar gwamnan da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Sanusi ya bayyana haka ne a wani bidiyo yayin jira da gidan jaridar BBC Hausa a yau Talata 20 ga watan Janairun 2026.
Jita-jitar barin Abba Kabir NNPP zuwa APC
Duka wannan bayani ya biyo bayan rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir zai bar NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Wannan mataki ya rikita siyasar Kano da kuma lalata alakar da ke tsakanin gwamnan da mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.
An samu rarrabuwar kawuna a tsakanin mabiya Kwankwasiyya yayin da wasu ke bin jagora wasu ko sun tare kusa da gwamna Abba Kabir.

Source: Facebook
Hadimin Abba ya magantu kan siyasar Kano
Yayin hirar, Sanusi ya ce babu wata matsala tsakanin Abba Kabir da mai gidansa a halin da ake ciki.
"Tun da aka kafa gwamnati mai girma gwamna yana zuwa wurin jagora yana kai masa ziyara, yana zuwa a kan idon mutane ko shi da shi, wannan ba sabon abu ba ne.
"Ko wani abu ba na labari ba ne, abin da na sani alakarsu tana nan mai karfi, domin alakarsu ba ta siyasa ba ce kadai.
"Alaka ce ta zamantakewa ta yan uwantaka da aiki da siyasa da komai da komai, alaka ce ta sama da shekaru 40."
Alakar da ke tsakanin Abba da Rabiu Kwankwaso
Sanusi Bature ya kuma yi karin haske kan alakar da ke tsakanin jagora da yaronsa Abba Kabir inda ya ce alakar ta wuce maganar siyasa.
Ya kara da cewa maganar rigima tsakaninsu ya yi wuri a tattauna sai dai idan an kai gabar sanin wani hukunci duka suka dauka.
Ya kara da cewa:
"Siyasa ba za ta zo ta bata ta ba, saboda bata fara da siyasa ba kuma ba za ta kare da siyasa ba, amma hukuncin da suka dauka a gaba shi zai iya tantance ko shin sun dauki hukunci iri daya ko kowa ya dauki nasa."
Abba Kabir ya roki alfarma wurin Tinubu
A wani labarin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja domin neman goyon bayansa a wasu bangarori.
Taron ya gudana ne a yayin da jita-jitar sauya shekarsa zuwa APC ke kara yaduwa da ke kara rikita siyasar jihar.
An ce Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Abba Yusuf cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta hada kai da Kano wajen magance matsalar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

