Shehu Sani Ya Gano Dalilin Jan Kafar Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya tofa albarkacin bakinsa kan batun sauya shekar Abba Kabir Yusuf zuwa APC
- Shehu Sani ya bayyana cewa sabanin yadda ake sauya sheka cikin sauki a wasu jihohi, lamarin Kano ya bambanta da saura
- Tsohon sanatan ya bayyana cewa tun asali siyasar Kano ta kasance ciki take da sarkakiya wanda sai jarumin namiji ne zai iya nasara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan batun sauya shekar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
Shehu Sani ya bayyana dalilan da suka sa Gwamna Abba ke jan kafa kan batun da ake ta rade-radi na sauya shekarsa, sabanin yadda ake ganin sauya shekar ‘yan siyasa a sauran jihohin kasar nan.

Source: Facebook
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.
Me Shehu Sani ya ce kan sauya shekar Abba?
Shehu Sani ya ce siyasar Kano tana da sarkakiya matuka, kuma ta ginu ne bisa dogon tarihi na rikice-rikice da hamayya, lamarin da ke sanya duk wani motsi na siyasa a jihar ya zama mai wahala.
“Duk sauya shekar da ake yi a kasar nan suna tafiya cikin sauki, sai dai na Kano kadai. Siyasar Kano har yanzu tana da zafi kamar yadda take a shekarar 1979.”
- Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya tuna baya
Shehu Sani ya tuna da rikice-rikicen siyasa na Jamhuriya ta Biyu, inda ya bayyana yadda rikicin akida da rabuwar kawuna suka girgiza siyasar tsofaffin jihohin Kano da Kaduna.
“Mu shaidu ne kan rikicin da ya faru a wancan lokacin. Lokacin da jam’iyyar PRP ta lashe zabe a Kano da Kaduna, mun rika jan masara a titunan Kaduna, masara tana cikin tambarin jam’iyyar NPN mai mulki a wancan lokaci.”

Kara karanta wannan
Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar
- Shehu Sani
Ya kara da cewa rabuwar kai da ta afku a cikin jam’iyyar PRP a wancan lokaci ta yi kama da rudanin siyasar da ake fuskanta a Kano a halin yanzu, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke fuskantar matsin lamba kan makomarsa ta siyasa.
“Lokacin da PRP ta kasu kashi-kashi, mun shiga rudani, ba mu san bangaren da za mu mara wa baya ba, ko na Malam Aminu Kano ko na Michael Imoudu da Alhaji Abba Rimi ke jagoranta."
- Shehu Sani
Fafatawar jam'iyyun NPN da PRP a 1981
Ya ce marigayi Gwamnan Jihar Kaduna, Balarabe Musa, ya yi kokarin jagorantar masu kishin ci gaba a tafiyar, har sai da aka tsige shi daga mukami, abin da ya bayyana a matsayin wani babban sauyi da ya karya gwiwar magoya bayan tafiyar.
“Balarabe Musa ya yi kokarin shawo kan lamarin a Kaduna har zuwa lokacin da aka tsige shi; daga nan gwiwoyin kowa suka yi sanyi."
- Shehu Sani

Source: Twitter
Da yake kwatanta wancan lokaci da halin da ake ciki yanzu, Shehu Sani ya ce siyasa kullum “fasaha ce ta tsallake kalubale,” wadda ke bukatar jarumta da juriya daga masu shiga cikinta.
“Siyasa galibi hanya ce ta wucewa daga wannan kalubale zuwa wani. Kana bukatar zuciya mai kwari domin jure matsin lamba da damuwa."
- Shehu Sani
NNPP ta magantu kan sauya shekar Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi magana kan shirin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na sauya sheka zuwa APC.
Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta yi nasarar lashe zaben gwamna a 2027 ko da kuwa Gwamna Abba ya fice daga cikinta.
Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya ce jam’iyyar ba ta damu da wannan yiwuwar sauya shekar ba, yana mai cewa NNPP ta riga ta kafa ingantaccen tsari a jihar Kano wanda zai ba ta damar cin zabe a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

