2027: Shirin da Kwankwaso Ke Yi Yayin da Gwamna Abba Ke dab da Shiga APC

2027: Shirin da Kwankwaso Ke Yi Yayin da Gwamna Abba Ke dab da Shiga APC

  • Ana ci gaba da batun sauya shekar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara duba mafitarsa kan matakin da zai dauka na gaba idan gwamnan ya fice
  • Majiya mai tushe ta bayyana mutanen da Kwankwaso yake tattaunawa da su daga jam'iyyu daban-daban domin fuskantar babban zaben shekarar 2027

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano -Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na tattaunawa da 'yan adawa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na gudanar da tattaunawa da manyan jagororin adawa a fadin ƙasar nan, domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

Kwankwaso na tattaunawa da 'yan adawa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wata majiya mai ƙarfi daga cikin makusantan Kwankwaso ta tabbatarwa da jaridar Leadership hakan.

Kara karanta wannan

Harin tikitin ADC ya kara zafi, tsohon Minista ya ayyana shirin neman shugaban kasa a 2027

Rabiu Kwankwaso na tattaunawa da 'yan adawa

Majiyar ta bayyana cewa tsohon gwamnan na Kano yana tattaunawa da shugabannin ADC, tsohon ɗan takarar shugaban kasa Peter Obi, da kuma tsohon ministan sufuri kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa, Chibuike Rotimi Amaechi.

Majiyar ta kuma ce Kwankwaso na tattaunawa da jam’iyyar PDP da sauran manyan ’yan adawa, da nufin gina haɗaka mai ƙarfi da za ta iya kalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a bainar jama’a, ta bayyana cewa:

“Kwankwaso ɗan siyasa ne. Yana magana da kowa. Ina da tabbacin yana tattaunawa da mutanen ADC, yana magana da Peter Obi, yana magana da Amaechi, kuma yana magana da PDP."
"Muna tattaunawa ne domin a haɗa dukkan ’yan adawa wuri guda."

Olusegun Obasanjo na tare da 'yan adawa

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo na daga cikin mutanen da ke goyon bayan yunƙurin haɗa kan 'yan adawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta hango lam'a a kalaman Kwankwaso na tilasta wa masoyansa koma wa APC

Ta bayyana cewa cewa wasu fitattun ’yan Najeriya da dama sun yi imanin cewa gwamnatin yanzu ba ta yi abin da jama’a suka yi zato ba.

Kwankwaso ya fara shirin tunkarar zaben 2027
Tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon Salim Sani Umar
Source: Facebook

Majiyar ta kara da cewa:

"Ba Obasanjo kaɗai ba ne. Kusan dukkan shugabannin Najeriya sun amince cewa ana bukatar sauyin gwamnati."
"Kowa na ganin cewa wannan gwamnati ba ta yin abin da ya dace. Abin da ya sa ake yawan ambaton Obasanjo shi ne saboda shi ne kaɗai ke faɗin ra’ayinsa a fili ba tare da tsoro ba.”

Kwankwaso ya yabawa 'yan Kwankwasiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kwararo yabo ga magoya bayansa.

Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya kasance tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya yabawa matasan da ke fafutukar kare akidun Kwankwasiyya a kafafen sada zumunta.

A cikin wani sako da ya fitar, Kwankwaso ya ce yana mika godiya ta musamman ga dakarun kafafen sada-zumunta na Kwankwasiyya, magoya baya da dukkan masu yi musu fatan alheri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng