Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Ganawar Bola Tinubu da Gwamnan Kano
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yuauf a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Fadar shugaban kasa ta tabbatar da ganawar Bola Tinubu da gwamnan Kano a wasu sakonni biyu da ta fitar a daren yau Litinin, 19 ga Janairu, 2025
- Wannan dai na zuwa ne yayin da ake rade-radin Gwamna Abba na shirye-shiryen sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Da yammacin yau Litinin, 19 ga watan Janairu, 2026 ne Gwamna Abba ya kai ziyara fadar shugaban kasa, inda ya gana da Bola Tinubu kan wasu muhimman batutuwa.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya gana da Gwamna Abba
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mai taimaka wa Bola Tinubu na musamman kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ya tabbatar da ganawar Abba da shugaban kasa.
"Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadarsa dazu da yamma." in ji shi.
Haka nan kuma mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da ganawar shugabannin biyu, inda ya wallafa hotunan da suka dauka bayan kammala tattaunawa.
Tinubu da Abba sun gama da tattaunawa
A gajeren sakon da ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar Litinin, Onanuga ya nuna cewa Tinubu da Abba sun kammala tattaunawa, duk da dai ban bayyana abin da suka maida hankali a kai ba.
"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kenan da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bayan wata ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin."
Duk da wannan tabbaci da aka samu daga fadar shugaban kasa, har yanzu babu wani bayani a hukumance da ya bayyana abin da suka tattauna a zaman.
Me ya kai Abba wurin Shugaba Tinubu
Ana kyautata zaton cewa wannan ganawa ta sirri da Tinubu ya yi da Abba Gida-Gida, ba zata rasa nasaba da shirye-shiryen gwamnan na ficewa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Waai majiyoyi sun yi zargin cewa Abba ya je wurin Bola Tinubu ne domin karkare tattaunawa kan bukatun da gwmanan ya gabatar kafin ya yarda ya shiga APC.
Rahotanni sun muna cewa Abba ya bukaci APC ta masa alkawarin ba shi tikitin takara babu hamayya a zaben 2027, lamarin da aka ce shi ne ya jinkirta komawa APC.

Source: Facebook
Gwamna Abba zai karbi katin zama dan APC
A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na iya karbar katin zama cikakken 'dan APC daga nan zuwa ranar Laraba.
Ya ce suna sa ran tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Abba su dawo Kano domin kaddamar da aikin fara rijistar 'ya'yan jam'iyya.
Ya kuma tabbatar da cewa idan Gwamna Abba ya shigo APC, shi ne zama jagoran jam'iyyar a jihar Kano yayin da Ganduje zai zama kamar uban jam'iyya.
Asali: Legit.ng

