Rashin Sa Hoton Kashim Shettima Ya Rikita Taron APC, Kakakin Majalisa Ya Harzuka
- Rashin sanya hoton Kashim Shettima a taron masu ruwa da tsakin APC na Arewa maso Gabas ya sake tayar da kura
- Kakakin Majalisar dokokin jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya nuna bacin ransa a wurin taron, wanda ke gudana a Maiduguri
- Mahalarta taron sun amince da maganganun da kakakin Majalisar ya yi, wanda ya ce masu shirya taron ba su yi adalci ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Rikicin APC a Kudu maso Gabashin Najeriya na neman dawowa kan kokarin raba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.
Rahotanni sun nuna cewa rashin sanya hoton Shettima a babbar banar da ke kunshe da manyan jagororin APC a shiryyar ya harzuka wasu mahalarta taron APC a jihar Borno.

Source: Twitter
Kakakin Majalisa ya soki cire hoton Shettima
Daily Trust ta rahoto cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, ya nuna rashin amincewarsa kan rashin ganin hoton Shettima a cikin banar bana a taron APC.
Babbar banar dai na dauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin APC guda biyar na Arewa maso Gabas, da kuma mai bada shawara kan shari'a na jam'iyyar.
Kakakin majalisar ya bayyana cewa rashin adalci ne masu shirya taron su buga bana ba tare da hoton mataimakin shugaban kasa ba, musamman ganin cewa ana gudanar da taron ne a garin da ya fito.
Abin da rashin sa hoton Shettima ya jawo
Haka kuma, ya tuna cewa irin wannan rashin sanya hoton ne ya janyo rudani da ya dagula taron APC a jihar Gombe a shekarar da ta gabata.
Hon. Abdulkarim ya ce:
"Wannan shi ne abin da ya janyo tarzoma a Gombe, kuma ga shi yana sake faruwa a nan Borno. Ban san manufar masu shirya taron ba, amma hakan bai dace ba.
"Ta yaya masu shirya taron za su cire hoton mataimakin shugaban kasa mai ci, wanda dan jihar Borno ne kuma dan shiyyar Arewa maso Gabas?"
Jama’ar da ke wurin sun mara wa korafin nasa baya, inda suka amsa da tafi mai karfi don nuna rashin amincewa da cire hoton Shettima, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Source: Twitter
Wane taro APC ta shirya a Maiduguri?
A halin yanzu, gwamnoni da masu ruwa da tsaki na APC sun taru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin taron jin ra’ayin jama’a na shiyyar Arewa maso Gabas kan gyaran kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Wannan taron yana daya daga cikin jerin tarurrukan da APC ke gudanarwa a shiyyoyin kasar nan don tattauna batutuwan da suka shafi tsarin mulkin jam'iyyar da kuma shirin zaben 2027.
An gargadi Tinubu kan canza Shettima
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar matasan APC ta gargadi Shugaba Bola Tinubu kan shirin maye gurbin Kashim Shettima da wani Kirista daga Arewa a zaben 2027.
Shugaban kungiyar, Kabiru Kobi, a hira da Legit Hausa ya bayyana cewa kokarin sauya Shettima zai iya kawo cikas ga nasarar Tinubu a zaben 2027.
Wannan gargadin ya biyo bayan rahotom da ya nuna cewa ana duba wasu jiga-jigan Kiristoci hudu a Arewa don zabar abokin takarar Tinubu daga cikinsu.
Asali: Legit.ng

