Aikin Gama Ya Gama, Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnan Kano a Abuja
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya isa fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja da yammacin yau Litinin, 19 ga watan Janairu, 2025
- Rahotanni sun ce yanzu haka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba sun shiga ganawar sirri domin tattauna wasu batutuwa
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin Gwamna Abba da mukarrabansa na shirin ficewa daga NNPP zuwa APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai ziyara fadar shugaban kasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu yan shiga wata ganawar sirri da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Tinubu ya sa labule da Gwamna Abba
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ganawar tana gudana ne a ofishin shugaban kasa da ke Aso Rock Villa a Abuja yau Litinin, 19 ga watan Janairu, 2025.
An tattaro cewa gwamnan na Kano, wanda aka gani sanye da farar babbar riga da jar hula, ya isa fadar shugaban kasa ne da misalin karfe 4:10 na yammacin yau.
An dade ana rade-raden shirin sauya shekar gwamnan daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Wane hali ake ciki kan sauya shekar Abba?
Sai dai, rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta tsaya cik saboda rashin yanke shawara kan ko za a ba shi tikitin takara kai tsaye a zaben 2027 ko a’a.
Shirin sauya shekar Abba ya kwashe makonni yana yawo a kafafen yada labarai, lamarin da ya janyo rashin jituwa tsakanin magoya bayansa da kuma ubangidansa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Idan za a iya tunawa, jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya riga ya karyata rahotannin da ke cewa ya amince ko ya goyi bayan shirin sauya shekar gwamnan na jihar Kano.
Sai dai duk da haka majiyoyi da dama sun yi ikirarin cewa Gwamna Abba ya riga ya yanke shawara, kuma babu abin da zai hana shi sauya sheka zuwa APC.

Source: Twitter
Dalilin ganawar Abba da Tinubu
Bayanai sun nuna cewa Gwamna Abba ya so tafiya kasar wajen domin ganawa da Tinubu, wanda ya tafi hutu tun karshen watan Disamba, 2025.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa daga baya gwamnan ya soke tafiyar bisa wasu daga dalilai da ba a bayyana ba, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Ana kyautata zaton cewa wannan ganawa ta yau bayan dawowar Tinubu Najeriya, ba za ta rasa nasaba da shirin sauya shekar Gwamna Abba ba.
Tinubu ya dakatar da rijistar APC a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya bayar da umarnin dakatar da fara aikin rijistar mambobin jam’iyyar APC ta intanet a Jihar Kano.
Dan Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo na daƙiƙu 27 da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Doguwa ya nuna cewa wannan mataki na da alaka da shirin tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda zai sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng

