Harin Tikitin ADC Ya Kara Zafi, Tsohon Minista Ya Ayyana Shirin Neman Shugaban Kasa a 2027
- 'Yan siyasar da ke da burin tsayawa takara a babban zaben shekarar 2027 na ci gaba da fitowa suna bayyana kujerun da za su nema
- Masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ADC sun kara yawa bayan tsohon karamin Ministan ilimi ya shiga jerinsu
- Emeka Nwajiuba wanda ya kasance tsohon dan majalisar wakilai ne, ya shiga cikin sahun mutanen da ke neman samun tikitin ADC don takarar shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gabanin zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027, tsohon karamin Ministan Ilimi kuma tsohon ɗan majalisar wakilai. Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.
Emeka Nwajiuba ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC mai adawa.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga ofishinsa da aka fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.
Emeka Nwajiuba zai nemi takara a ADC
Da yake magana kan burinsa, Nwajiuba ya jaddada cewa ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu na buƙatar shugabanci mai dogaro da tsare-tsare bayyanannu.
Ya ce akwai bukatar samun shugabanci mai inganci, da kuma ingantaccen tsarin siyasa tun daga matakin tushe, ba wai a magana kawai ba, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Sanarwar ta ce shekarunsa a majalisa, reshen zartarwa na gwamnati, da kuma muhimman cibiyoyin kasa sun ba shi cikakkiyar fahimta kan shugabanci da kula da kuɗaɗen gwamnati.
Ana sa ran tsohon ministan zai mayar da hankalin yaƙin neman zaɓensa kan gyaran harkar ilimi, daidaita tattalin arziki, da sake gina amincewar jama’a ga cibiyoyin gwamnati.
'Yan takara za su nemi kujerar shugaban kasa
Shigarsa takarar a ƙarƙashin jam’iyyar ADC na kara wani sabon salo ga gasar neman shugabancin kasa, musamman a lokacin da ƙananan jam’iyyu ke kokarin gabatar wa ’yan Najeriya sabon zabi da ya bambanta da gwamnatin yanzu.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi martani da dansa ya sauya sheka zuwa APC, zai goyi bayan tazarcen Tinubu
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Nwajiuba, kwararren lauya ne da ya yi rantsuwar kama aiki a Najeriya a shekarar 1989, kuma tsohon shugaban kwamitin gudanarwa na asusun tallafawa ilimi na manyan makarantu (TETFund)."
"Ya shiga takarar da saƙon da ya gina a kan abin da ya kira tsarin shugabanci na ‘fifita ƙwarewa’. Bayyanarsa ta nuna shigowar ɗan takara da ke sanya kwarewa, zurfin manufofi, da sanin aiki a cibiyoyi a tsakiyar tafiyar da harkokin kasa.”
“Da wannan sanarwa, Nwajiuba ya shiga jerin ’yan takarar da ke karuwa waɗanda ke neman tsara tattaunawar kasa gabanin babban zaɓe mai zuwa, yayin da muhawara kan kwarewa, gogewa, da shugabanci mai haɗa kai ke ci gaba da ƙara ɗaukar hankali.”

Source: Facebook
ADC ta samo hanyar ceton Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi tsokaci kan batun ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa manufar jam’iyyar adawar ita ce kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki.
Kakakin na ADC mai hamayya ya bayyana cewa abin da jam'iyyar ta tasa a gana shi ne raba Shugaba Tinubu da mulki don ceto Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
