'APC za Ta Fadi a 2027,' An Aika wa Tinubu Sakon Shan Kaye a Zabe Mai Zuwa
- Mai neman takarar shugaban kasa a PDP, Gbenga Olawepo-Hashim, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta rasa mulki a zaben 2027 ta hanyar kuri’ar jama’a
- Ya zargi jam’iyya mai mulki da kawo matakan da ke nufin raunana 'yan adawa, yana mai cewa hakan ba zai rushe tsarin dimokuradiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya ba
- Olawepo-Hashim ya yi kira ga ’yan Najeriya da kasashen duniya su sa ido tare da kare ka’idojin dimokuradiyya domin hana kasar zuwa tsarin mulkin jam’iyya daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja — Tsohon mai neman shugaban kasa a PDP, Gbenga Olawepo-Hashim, ya ce duk da matsalolin shari’a da kuma matsin lamba da jam’iyyun adawa ke fuskanta, APC ba za ta tsira daga faduwa a zaben 2027 ba.
Gbenga Olawepo-Hashim ya ce ’yan Najeriya za su yi amfani da kuri’arsu wajen canza gwamnati cikin lumana da bin doka da oda.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Olawepo-Hashim ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyyar da aka shimfida tun farkon kafuwar Najeriya ba zai rushe ba.
APC za ta fadi a 2027 inji Olawepo-Hashim
A cikin jawabin nasa, Olawepo-Hashim ya zargi jam’iyyar APC da daukar matakai da ke nufin rage karfin jam’iyyun adawa kafin shiga sabon zangon zabe.
Ya bayyana wadannan matakai a matsayin abin damuwa, yana mai cewa suna kama da yunkurin da aka taba gani a baya na dakile bambancin ra’ayi da siyasa.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa ya ce irin wadannan dabaru ba su taba yin nasara ba a tarihin siyasar Najeriya, domin jama’a kan tashi tsaye su kare hakkinsu idan aka nemi tauye musu damar zabe da fadin albarkacin baki.
A kan haka Olawepo-Hashim ya bayyana cewa duk da abubuwan da suke faruwa jam'iyyar APC za ta sha kaye a zaben shekarar 2027.
Kira ga ’yan Najeriya da kasashen waje
Olawepo-Hashim ya bukaci ’yan Najeriya da kuma kasashen duniya su kasance masu sa ido da taka-tsantsan wajen kare dimokuradiyya.
A bayanin da ya yi, dan siyasar ya ce kare tsarin zabe da tabbatar da gaskiya na bukatar bin doka, gaskiya da rikon amana daga dukkan bangarori.
Ya kammala da bayyana kwarin gwiwarsa cewa a 2027, ’yan Najeriya za su zabi sauyi ta hanyar kada kuri'a, inda za su kori APC daga mulki cikin lumana, tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta ci gaba da kafuwa a kasar.
Jam'iyyar APC ta yaba wa Atiku
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta fito karara ta yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar.
Legit Hausa ta rahoto cewa APC ta yi magana ne kan matakin da Atiku ya dauka bayan dansa ya fita daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki.
A martanin da Atiku ya yi, ya bayyana cewa ba ya tilasta wa mutane su bi wani ra'ayi na siyasa da ba su so domin dimokuradiyya ta ba su damar hakan.
Asali: Legit.ng

