Kungiyar Tallata Atiku Ta Kori Abba da Ya Rabu da Mahaifinsa Ya Koma APC
- Musa Bakari ya sanar da korar Abba Atiku Abubakar daga kungiyar Atiku Haske saboda sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Bakari, wanda ke shugabantar kungiyar ya bayyana cewa sun samu labarin Abba ya yi gaban kansa wajen canja wa kungiyarsu suna
- Kungiyar ta ce ba Abba ne ya kafa ta ba, kuma babu ko sisinsa a cikin tafiyar da harkokinta, saboda haka ya je sun kore baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Musa Bakari, wanda ya kafa kuma ke jagorantar kungiyar Atiku Haske, ya sanar da korar Abba Atiku Abubakar daga ƙungiyar, bayan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC.
A ranar Alhamis ne Abba, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, Atiku Abubakar, ya sauya sheƙa zuwa APC.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa bayan sauya sheƙar, Abba ya umarci mabiya tsarin siyasar da ke ƙarƙashinsa da su bi APC tare da fara tattara goyon baya ga manufar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar haske ta kori 'ɗan Atiku
Nigerian Tribune ta wallafa cewa kungiyar tallata Atiku ta haske ta sanar da sauya sunan tsarin nasa zuwa kungiyar Haske Bola Tinubu.
Sai dai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Bakari ya ce Abba ba shi da hurumin yanke shawarar siyasar kungiyar Atiku Haske.
Ya bayyana cewa ba Abba ne ya kafa ƙungiyar ba, don haka ba shi da ikon bayar da umarni kan jam’iyyar da ƙungiyar za ta mara wa baya ko ɗan takarar da za ta goyi baya.
“Mu ne mu ka kafa kungiyar Atiku Haske, kuma kawai muka gayyaci Abba ya shiga ƙungiyar,."
Bakari ya ƙara da cewa Abba bai taɓa bayar da ko sisi ɗaya ba wajen ayyukan ƙungiyar, kuma ba ya riƙe da takardar rajista ta ƙungiyar. Saboda haka, in ji shi, ba su da wani wajibci na bin umarnin da Abba ya bayar.

Kara karanta wannan
Waiwaye: Yadda ɗan Obasanjo ya goyi bayan Buhari shekaru kafin Abba Atiku ya koma APC
Kungiyar Atiku haske ta bi bayan ADC
Bakari ya ce, a maimakon haka, Abba shi ne ke ƙarƙashin dokokin ƙungiyar, kuma ya gaza cika ƙa’idojinta, lamarin da ya sa aka kore shi kai tsaye daga cikinta.
Ya jaddada cewa kungiyar Atiku Haske ba ta da sha’awar bin Abba zuwa kowace jam’iyya, kuma za su ci gaba da goyon bayan ADC.

Source: Facebook
Bakari ya ƙara da cewa ƙungiyar da a baya take cikin PDP, ta yanke shawarar komawa ADC gaba ɗaya, kuma abin da Abba ya yi ya saɓa wa kudurinsu, ƙimarsu da manufofinsu.
“Saboda haka, an kori Abba daga ƙungiyar."
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar na nan daram kan burinta na ganin an kafa gwamnati mai kyakkyawan shugabanci da rage wa ‘yan Najeriya radadin rayuwa.
“Mun ƙara tabbatar da cewa Mai Girma Atiku Abubakar shi ne mafi cancanta da zai kai mu ga cimma manufofinmu."
APC ta yaba wa Atiku Abubakar
A wani labarin, kun ji cewa APC ta yi watsi da rade-radin da ke cewa bayyana cewa sauya shekar Abba Atiku Abubakar daga jam’iyyar PDP zuwa cikinta na iya haddasa rikici ko girgiza jam’iyyar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa APC ta ginu ne a kan tsari, ladabi da ƙa’idoji masu ƙarfi, waɗanda ba za su bari mutum guda ya kawo ruɗani ko tarwatsa jam’iyyar ba, ko da wane ne shi.
APC ta kuma yaba wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa yadda ya nuna natsuwa da fahimta kan matakin da ɗansa ya ɗauka na sauya sheƙa zuwa APC.
Asali: Legit.ng

