Ganin Abba da Hular Kwankwasiyya, Tutar NNPP Ya Jawo Magana Yana Shirin Komawa APC

Ganin Abba da Hular Kwankwasiyya, Tutar NNPP Ya Jawo Magana Yana Shirin Komawa APC

  • Sauya shekar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jawo magana bayan ya gudanar da taron majalisar zartarwa a Abuja
  • An gano Abba Kabir sanye da hular Kwankwasiyya da tutar NNPP, lamarin da ya tayar da rade-radin sauya sheka
  • Taron ya gudana a Abuja tare da mataimakin gwamna da kwamishinoni, inda gwamnan ya jaddada bukatar hadin kai da fahimtar juna a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci taron farko na majalisar zartarwar jiha a bana a Abuja.

An gano gwamna Abba Kabir Yusuf sanye da hular ja ta Kwankwasiyya tare da tutar NNPP.

An gano Abba da jar hula ana rade-radin zai koma APC
Gwamna Aban Kabir a taron majalisar zartarwa. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Ana ce-ce-ku-ce kan maganar komawar Abba APC

Wannan bayyanar tasa ta janyo ce-ce-ku-ce, inda ake kallonta a matsayin sako ga rade-radin da ke yawo kan yiwuwar sauya shekarsa ta siyasa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Da gaske harkokin gwamnati sun tsaya cak a Kano Abba na shirin shiga APC?

An gudanar da taron ne a birnin Abuja, kuma dukkan kwamishinonin jihar sun halarta tare da Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam.

Mataimakin gwamnan ma na daga cikin sunayen da ake ambata a rade-radin sauyin siyasa da ake zargin na faruwa a shugabancin jihar Kano.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Abba ya bukaci mambobin majalisar zartarwa su kasance masu hadin kai, juriya da fahimtar juna a kowane lokaci.

Ya ce hadin kai a cikin gwamnati na da matukar muhimmanci wajen cimma muradun ci gaba da biyan bukatun al’ummar jihar Kano baki daya.

Gwamnan ya ce:

"Na bukace ku da ku ba wannan gwamnati cikakken hadin kai, mu kasance kamar iyali domin daukaka Kano.”

Ya kara da cewa dole ne a yi aiki da mutunta juna da fahimta domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Siyasar Kano ta dagule kan shirin barin Abba NNPP zuwa APC
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Abba ya fadi manyan tsare-tsaren gwamnatinsa

Bayyanarsa da kalaman da ya yi sun nuna cewa bai da niyyar sanar da sauya jam’iyya, sabanin hasashen da wasu ke yi.

Har ila yau, Gwamna Yusuf ya bayyana manyan tsare-tsaren ci gaban gwamnatinsa, musamman a bangaren karfafa matasa.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya fadi yadda Abba zai buga rikici da Ganduje

Ya ce gwamnatin jihar na shirin kaddamar da shirye-shiryen samar da ayyukan yi da koyon sana’o’i ga matasa a shekarar 2026.

A cewarsa, akalla matasa 50,000 ne za su amfana da wadannan shirye-shirye a fadin jihar Kano, cewar Daily Post.

Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da manufofin da za su bunkasa tattalin arziki da zaman lafiya.

Ya ce ana son ci gaba mai dorewa da shigar kowa cikin tafiyar mulki domin amfanin al’ummar Kano baki daya.

'Abin da ya jinkirta zuwan Abba APC'

Kun ki cewa shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka daga NNPP zuwa APC ya samu tangarda kan bukatar tikitin takara a 2027

Shugabannin APC sun ki amincewa da bukatar da aka ce gwamnan ya nema suna nacewa cewa dole gwamnan ya bi tsari.

Rikicin sauya shekar na kara tayar da jijiyoyin wuya a Kano, yayin da APC ke cewa gwamnan zai shiga jam’iyyar “a lokacin da ya dace”.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com