Idan Abba Ya Koma APC, Waye Sarkin Kano? ’Yan Majalisa Sun Yi Karin Haske
- Wasu ‘yan majalisar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Asabar 17 ga watan Janairun 2026
- ‘Yan majalisar sun fadi Sarkin Kano ko da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC duba da yadda tsarin doka yake
- Sun yi watsi da maganar haɗin Abba Kabir da Abdullahi Ganduje, suna cewa shi makiyin Kano ne, kuma ba za su bi Gandujiyya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu daga cikin yan majalisun jiha sun yi magana game da dambarwar da ke faruwa a jihar musamman bangaren siyasa a Kano..
Hon. MB Aliyu da Hon. Usman Kiru daga jihar Kano sun bayyana matsayarsu kan bangaren da za su bi a siyasance.

Source: Twitter
Legit Hausa ta leko wannan bayanin ne daga shafin YouTube na Fact News Hausa yayin hira da 'yan majalisun a jihar.

Kara karanta wannan
Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar
Matsayar wasu yan majalisar Kano kan rikicin siyasa
A cikin bidiyon, yan majalisar sun tabbatar da cewa suna tare da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.
Sun jadda aniyarsu ta kasancewa da shi saboda salon jagorancinsa inda suka ce suna kallonsa kamar mahaifi a gare su.
Har ila yau, yan majalisar sun yi magana game da shirin Abba Kabir na Kano zuwa jam'iyyar APC mai mulki daga NNPP.
Sun bayyana cewa ko da Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC, Sarki Muhammadu Sanusi II ne zai ci gaba da zama Sarki.
A cewarsu:
"Ah Sarkin Kano na yaya? tun da ai kowa ya san Sarki, kamar idan kika ce waye gwamnan Kano, kowa ya sani Abba Kabir ne har ranar zabe.
"Kowa ya sani Muhammadu Sanusi II shi ne Sarkin Kano domin duk mutumin jihar idan kika tambaye shi zai ce Sanusi Lamido Sanusi zai ce.
"Ko bincike aka yi a manhajar AI ko Google, duk zaki samu amsa, wannan shi ne magana ta gaskiya."

Source: Facebook
Yan majalisa sun soki hadakar Abba, Ganduje
Game da maganar tarayyar Abba Kabir da Abdullahi Ganduje a APC, yan majalisar suka ce aikin banza ne saboda zai ci karo da makiya.
"Can din su waye zai tarar? makiya ne a can, kowa ya san Ganduje makiyin jihar Kano na farko.
"Duk wani abin da jihar Kano za ta samu ci gaba su ba shi ne a gabansu ba, su burinsu shi ne su samu su da 'ya'yansu.
"Koda zamu yi APC ba za mu yi Gandujiyya ba, munanan a cikin Kwankwasiyya har yanzu."
- Cewar yan majalisar Kano
APC ta karyata maganar tikiti da Abba Kabir
Mun ba ku labarin cewa ana yada jita-jitar wai cewa Abba Kabir na neman a ba shi tikitin takara kai tsaye a zaben shekarar 2027.
Sai dai APC a Kano ta ce Gwamna Abba na kan hanyarsa ta shiga jam’iyyar, inda ta karyata rade-radin cewa an taba ganawa da shi kan tikitin takara kai tsaye.
Sakataren APC a Kano, Alhaji Zakari Sarina, ya ce jam’iyyar na maraba da gwamnan a kowane lokaci, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jita.
Asali: Legit.ng
