Bashir Ahmad Ya Taba Abba Kabir kan Tsawaita Maganar zuwa APC, Ya Fadi Illar Haka
- Ana zargin batun yiwuwar sauya shekar gwamnan Kano zuwa APC ya fara janyo tsaiko a tafiyar da mulki
- Bashir Ahmad ya ce ya dace a kammala shirye-shiryen a boye kafin fito da batun sauya sheka fili
- Ya gargadi cewa tsawaita rikicin siyasa na iya jefa Kano cikin matsin lamba da rashin tabbas da jihar ba ta bukata a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Bahir Ahmad ya magantu game da dambarwar siyasar Kano da ke faruwa.
Bashir Ahmad ya ce siyasar Kano tun fil’azal tana da wani salo na daban idan aka kwatanta da siyasar sauran sassan kasar nan.

Source: Facebook
Bashir Ahmad ya magantu kan siyasar Kano
Bashir Ahmad ya bayyana ra'ayinsa game da rikicin siyasar a yau Asabar 17 ga watan Janairun 2026 a shafin X.
Tun bayan da gwamnan jihar ya yi ishara makonni da suka wuce kan yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, an lura cewa harkokin mulki a jihar sun fara yin sanyi.
Dan siyasar ya ce hankalin gwamnati da na al’umma ya karkata ne gaba daya zuwa tattaunawar siyasa kan batun sauya shekar, lamarin da ke barazana ga ci gaban ayyukan gwamnati.
Ya bayyana cewa irin wannan muhimmin shawara ya dace a kammala ta a cikin gida ne, bayan an yi tuntuba da dukkan bangarori da abin ya shafa, kafin ta fito fili ga jama’a.
Bashir Ahmad ya yi nuni da cewa a jihohi da dama, gwamnoni sun sauya sheka zuwa APC ba tare da hayaniya ko rudani ba, domin an kammala komai tun kafin bayyanar labarin.
A cewarsa, tsawaita wannan batu a Kano ya haifar da tashin hankali da matsin lamba na siyasa da za a iya kauce musu, alhali jihar ba ta da damar jure irin wannan yanayi a halin da ake ciki.

Source: Twitter
Shawarar da Bashir Ahmad ya ba shugabanni
Bashir Ahmad ya bukaci shugabanni su maida hankali kan cika alkawuran mulki da kyakkyawan shugabanci, maimakon barin al’umma cikin yanayin rashin tabbas na siyasa.
"Siyasar Kano tun da dadewa tana da bambanci idan aka kwatanta da siyasar sauran jihohi, tun lokacin da gwamnan jihar ya yi ishara makonni da suka wuce game da yiwuwar sauya sheka zuwa APC, al’amuran mulki a jihar kamar sun fara ja baya, yayin da hankali ya karkata gaba ɗaya zuwa siyasar batun sauya shekar.
"Irin wannan shawara ya dace a kammala ta a cikin sirri ne, bayan an yi dukkanin shawarwari da masu ruwa da tsaki, kafin ta fito da shi fili, haka lamarin ya kasance a wasu jihohi, inda gwamnoni suka koma APC ba tare da hayaniya ko rudani ba."
Ya ce tsawaita wannan batu ya shafi tafiyar da mulki a Kano tare da haifar da tashin hankali da matsin lamba na siyasa da za a iya kauce wa su.
Kano: Kwamanda ya sha alwashin cin amanar APC
An ji cewa kusa a APC a jihar Kano, Abdulmajeed Almustapha Dan Bilki Kwamanda, ya soki jam’iyyarsa kan yadda take watsi da ’ya’yanta.
Kwamanda ya ce za su iya cin amanar APC idan aka hana Barau Jibrin taka rawa a 2027, yana mai cewa hakan zai jawo faduwarta.
Dan siyasa ya kuma caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf, yana zarginta da almundahana, tare da yabon Barau Jibrin.
Asali: Legit.ng

