Gwamna Dauda Lawal Ya Mika Wasikar Komawa APC? Jam’iyyar Ta Yi Karin Haske
- Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta yi martani game da rahoton cewa Gwamna Dauda Lawal zai sauya sheka daga PDP a ranar Asabar
- APC ta bayyana rahoton a matsayin kirkirarre da yaudara, tana zargin wasu da yada labaran karya domin tayar da hankula
- Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da al’ummar Zamfara su yi watsi da rahoton, tana cewa babu wata alama ta ficewar gwamnan daga PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta yi magana game da rahoton cewa Gwamna Dauda Lawal ya mika wasikar sauya sheka domin shiga jam’iyyar.
Jam’iyyar APC ta bayyana labarin a matsayin kirkirarre kuma na yaudara, tana cewa ba shi da tushe balle makama.

Source: Facebook
APC ta musanta sauya shekar Dauda Lawal
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na APC a Zamfaraya, Malam Yusuf Idris ya fitar wanda jaridar Punch.
Yusuf Idris ya ce rahoton da ake cewa ya fito daga Tambarin Gusau karya ne tsagwaron gaske, kuma an kirkiro shi ne da muguwar manufa.
A cewarsa, rahoton abin takaici ne, mara tushe kuma cike da sharri, yana zargin masu yada shi da ganganci wajen yaudarar jama’a da kuma haddasa tashin hankali a cikin jam’iyyar.
Ya ce:
“Jam’iyyar APC a Zamfara ta ci karo da wani rahoto na karya da ake cewa ya fito daga Tambarin Gusau, wanda ke ikirarin cewa Gwamna Dauda Lawal ya aike da wasika yana nuna sha’awarsa ta shiga APC.”

Source: Original
APC ta ja kunnen 'ya'yanta a Zamfara
Idris ya jaddada cewa APC jam’iyya ce da ke aiki ta hanyoyi da ka’idoji na hukuma, inda ya ce babu irin wannan wasika da jam’iyyar ta karba daga gwamnan.
“Jam’iyyar ba ta karbi wata wasika daga Gwamna Dauda Lawal kamar yadda ake ikirari ba, haka kuma APC ba ta da labarin wani sabon yunkuri daga gwamnan na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.”
- Yusuf Idris
Mai magana da yawun jam’iyyar ya bukaci mambobin jam'iyyar APC da kuma al’ummar Jihar Zamfara gaba daya da su yi watsi da rahoton baki daya, yana mai bayyana shi a matsayin tunanin wasu da aka kirkira domin jefa mutane cikin rudani.
Ya ce makasudin labarin shi ne tayar da hankali da rikitar da al’amura ba tare da wani dalili na gaskiya ba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta da hannu a irin wannan labari na karya, cewar Daily Post.
'Yan majalisar Zamfara sun koma PDP
A baya, an ji cewa jam'iyyar APC mai adawa a Zamfara ta gamu da cikas bayan wasu mambobinta guda biyu a majalisar dokokin jiha sun yi murabus daga cikinta.
Mambobin guda biyu sun sanar da raba gari da APC ne a cikin wasiku daba-daban da suka aikawa shugaban majalisar dokokin, Bilyaminu Moriki.
Sun bayyana cewa lokaci ya yi da za su yanke alakar da ke tsakaninsu da APC saboda abin da suka kira rashin jagoranci mai kyau a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

