Shiga APC: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Abba zai Buga Rikici da Ganduje

Shiga APC: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Abba zai Buga Rikici da Ganduje

  • Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na ci gaba da karɓar ‘yan siyasa a gidansa da ke Kano, inda suke jaddada masa biyayya
  • Kwankwaso ya ce ko da Abba Kabir Yusuf ya shiga APC, da kyar a samu zaman lafiya tsakaninsa da jagoran APC na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Tsohon gwamnan ya aike da sakon gargadi ga ‘yan majalisar Kano da ‘yan NNPP, yana kira gare su da su tsaya tsayin daka su guji rudanin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na ci gaba da karɓar manyan ‘yan siyasa da magoya bayansa a gidansa da ke Kano, inda suke nuna goyon baya gare shi a wani yanayi da siyasar jihar ke kara ɗaukar sabon salo.

Kara karanta wannan

An samu matsala a shirin ganawar gwamnan Kano da Tinubu kan batun komawa APC

Wannan na faruwa ne yayin da ake rade-radi cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na iya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje, Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Salihu Tanko Yakasai|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Kwankwaso ya yi ne a wasu jerin sakonni da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a sahfinsa na Facebook.

Zaman da Abba zai yi da Ganduje

Kwankwaso ya yi tsokaci kai tsaye kan maganar shigar Abba APC, yana mai cewa ko da gwamnan ya sauya sheka, samun fahimta ko zaman lafiya tsakaninsa da jagoran APC na Kano, Abdullahi Umar Ganduje, zai yi matukar wahala.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa abubuwan da gwamnan Kano ya fito ya fada a bainar jama’a a baya sun nuna bambancin siyasa mai zurfi tsakaninsa da Ganduje.

Ya ce gwamnan ya fito ya bayyana abubuwan da aka yi da kuma wadanda ba a samu damar yi ba a lokacin da suka gabata, ciki har da ayyukan cibiyoyin koyon sana’o’i da suka amfanar da jama’a a fadin jihar Kano.

Ya ce:

"Ni na sani musamman ma kuna jin abin da gwamna ya ce kwanan nan, gwamna ya fito da wadancan mutanen tsirara, ya fadi abubuwan da suka yi da abubuwan da suka kasa yi a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya fadi yadda Abba Kabir ya tona asirin Ganduje

"Sun fito sun fada cewa abin da muka yi a cibiyar koyon sana'a abin sha'awa ne, wace unguwa ce, wane gida ne a nan jihar Kano da za ka ce na kusa da kai ko naka ko kai kanka ba a amfana ba, wannan magana da ya yi, ina jin ko ya shiga zaman doya da manja za su yi."

A wani bangare na jawabin nasa, Kwankwaso ya aike da sakon jan hankali ga ‘yan majalisar Kano, yana mai cewa a irin wannan lokaci ya dace su zama ‘yan gwagwarmaya na gyara da kare muradun jama’a.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na bayani. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

'Abba ya tona asirin Ganduje,' Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa Abdullahi Umar Ganduje gugar zana yayin wani taro a jihar Kano.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce Abba Kabir Yusuf ya tona asirin Abdullahi Ganduje da ya fadi wasu abubuwan da ya gaza yi a lokacinsa.

Yayin wani taro a Kano, Abba Kabir ya ce gwamnatin Ganduje ta rufe wajen koyon sana'o'i da Kwankwaso ya samar a jihar a shekarun baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng