2027: Jihohin Arewa 19 Za Su Tsaida Wanda Za Su Zaba tsakanin Tinubu da Atiku

2027: Jihohin Arewa 19 Za Su Tsaida Wanda Za Su Zaba tsakanin Tinubu da Atiku

  • Wata kungiyar Arewa, RAID ta sanar da cewa jihohin shiyyar 19 za su sanar da dan takararsu na shugaban kasa a taron da za a yi a Afrilu, 2026
  • Babban taron Arewa da za a gudanar zai haɗa kan shugabannin gargajiya da na siyasa domin samar da mafita kan tsaro da ci gaban shiyyar
  • RAID ta gargaɗi gwamnati kan rashin hukunta masu laifi da rashin aiwatar da manufofin ilimi waɗanda ke janyo ta'addanci a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata ƙungiyar kare muradun Arewa mai suna RAID, ta yi magana game da wanda daukacin jihohi 19 na shiyyar za su zaba shugaban kasa a 2027.

Kungiyar RAID ta bayyana cewa, a watan Afrilun wannan shekara ta 2026, za su fitar da matsayar jihohin Arewa kan ɗan takarar shugaban ƙasa da za su marawa baya.

Kara karanta wannan

ADC: Momodu ya kare Atiku kan zargin shirin amfani da kuɗi wajen sayen takara

Arewa za ta gudanar da tro na zabar dan takarar shugaban kasa a 2027
Peter Obi (hagu), Atiku Abubakar (tsakiya) da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (dama). Hoto: @PeterObi, @atiku, @officialABAT
Source: Twitter

Arewa za ta yi taro gabanin 2027

Wannan sanarwa ta fito ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar a Abuja ranar Juma'a, 16 ga Janairu, 2026, cewar rahoton Vanguard.

Kungiyar RAID ta jaddada cewa yankin Arewa na fuskantar ƙalubale masu sarkakiya waɗanda ba za a iya magance su da yin shiru ko rarrabuwar kai ba.

Daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar, Comrade Bitako Abubakar Umar, ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron Arewa a watan Afirilu wanda zai haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki.

Taron zai ƙunshi shugabannin siyasa, na gargajiya, da na addini; kungiyoyin matasa da mata; da kuma kungiyoyin farar hula da ƙwararru a fannoni daban-daban.

Manufar taron ita ce samar da tsari ɗaya wanda zai jagoranci zaɓin shugabanni da alkiblar manufofin siyasa gabanin zaɓen 2027 domin Arewa ta tafi da murya ɗaya wajen tattaunawa da sauran sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Fitacciyar mawakiyar yabon addini ta riga mu gidan gaskiya

Matsalar tsaro da tabarbarewar ilimi

Ƙungiyar ta nuna matsananciyar damuwa kan yadda rashin tsaro ya addabi Arewa, wanda ya haɗa da fashin daji, ta'addanci, da garkuwa da mutane, in ji rahoton The Sun.

Umar ya bayyana cewa samun rauni a bangarorin da ke hukunta masu laifi da kuma ci gaba da biyan kuɗin fansa sune ke ƙara rura wutar ta'addanci a yankin.

Haka kuma, ya soki rashin aiwatar da tsarin ilimin bai-ɗaya na (UBE), wanda hakan ya janyo ƙaruwar yara da ba sa zuwa makaranta.

Wadannan yara, a cewarsa, sune ƙungiyoyin masu laifi ke amfani da su cikin sauƙi don ayyukansu na ta'addanci.

An ce taron zai hada da sarakunan Arewa, 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki na shiyyar.
Sarakunan Arewa, ciki har da sarkin Musulunci, Alhaji Sa'ad Abubakar a wani taro a Kaduna. Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Buƙatar haɗin kai a Arewa

RAID ta jaddada cewa rashin hadin kan 'yan siyasa da wadanda ake mulka da rashin adalcin masu mulki na tsawon lokaci ne suka rura wutar rashin jin daɗi a Arewa.

Don haka, babban taron na watan Afirilu zai zama wani dandamali da ba na siyasa ba, inda za a tattauna yadda za a dawo da zaman lafiya, yaƙi da talauci, da kuma inganta harkokin mulki a duk faɗin jihohin Arewa 19.

Kara karanta wannan

Borno: Tsohon ɗan takarar gwamna ya yi watsi da PDP, ya rungumi ADC gabanin 2027

Kungiyoyin Arewa sun amince da tazarcen Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gamayyar kungiyoyi sama da 1,000 na Arewa sun yi taro a Abuja kan wanda ya dace su marawa baya a zaɓen 2027.

Shugaban gamayyar, Usman Abdullahi ya bayyana cewa tun da Najeriya ta samu ƴanci, ba a taɓa gwamnati mai aminci kamar ta Bola Tinubu ba.

A cewarsa, gwamnatin APC ta kawo canjin da ya farfaɗo da Arewa, yana mai jaddada goyon baya ga tikitin Tinubu/Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com