ADC: Momodu Ya Kare Atiku kan Zargin Shirin Amfani da Kuɗi wajen Sayen Takara
- Dele Momodu, jagora a ADC ya ce ba gaskiya ba ne zargin cewa Atiku Abubakar zai yi amfani da kuɗi domin rinjayar zaɓen fitae gwani na ADC
- Ya jaddada cewa kuɗin kamfen ba cin hanci ba ne, illa wajibi ne domin gudanar da sahihin kamfen da kare ƙuri’u a ranar zaɓe idan ana son sakamako
- Babban 'dan jaridar kuma 'dan siyasa ya kawo misalin zaɓen shugaban ƙasa na Amurka na 2024 don nuna tarin kuɗi kaɗai ba ya tabbatar da nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja - Bashorun Dele Momodu, jigo a jam’iyyar hadaka, ya yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa game da zaɓen fitar da gwani na zaben Shugaban ƙasa a ADC.

Kara karanta wannan
"Abokin barawo": Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Gumi da masu goyon bayan 'yan ta'adda
Ya ce maganar cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai iya amfani da kuɗi domin rinjayar zaɓen jam’iyyar ta hanyar da ba ta dace ba, ba ta da tushe.

Source: Twitter
Dele Momodu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin wata hira da ya yi a shirin Morning Brief na gidan talabijin ɗin Channels Television, inda aka tattauna batun yadda ADC ke shirin tsayarda ɗan takara.
'Da bambanci tsakanin kudin takara da kamfen' - Momodu
Daily Post ta ruwaito cewa Mawallafin ujallar Ovation ya bayyana cewa akwai bambanci sosai tsakanin kuɗin kamfen da kuma cin hanci, yana mai cewa kuɗi wajibi ne domin aiwatar da sahihin tsare-tsaren kamfen da ayyukan ranar zaɓe.
A cewarsa:
“Ba wai kuɗi kawai ba ne. Idan muna magana a kan kuɗi, muna nufin harkokin dabaru da tsari. Ba muna magana ne kan ba da cin hanci ba.”
Ya ce ana amfani da irin waɗannan kuɗi wajen sufuri, tsaro, sa ido kan rumfunan zaɓe da kuma kare sakamakon ƙuri’u, amma wannan ba shi da alaka da cin hanci.
Momodu ya ƙara da cewa, a ranar babban zaɓe, jam’iyya na buƙatar tanadi domin tabbatar da cewa kowane rumfar zaɓe na da isasshen wakilci don da ido.
Ya ce:
"Kana buƙatar tabbatar da cewa babu wanda zai sace kuri'unka. Wannan ne abin da muke nufi idan muka ce kuɗi."
Momodu ya kawo misali da siyasar Amurka
Momodu ya kawo misalin zaɓen shugaban ƙasa na Amurka na 2024, inda ya ce duk da cewa Kamala Harris ta fi Donald Trump tara kuɗin kamfen, hakan bai hana ta faɗuwa ba.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ko a Amurka ma, Kamala Harris ta fi Donald Trump tara kuɗi. Ta samu sama da Dala biliyan ɗaya don kashewa, amma duk da haka ba ta yi nasara ba."
Dangane da maganar ƙarfin kuɗin Atiku, Momodu ya bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ba ya rike da ikon wata jiha ko albarkatun gwamnati.
Ya ce:
“Atiku ɗan kasuwa ne, kuma ya kasance ɗan kasuwa tun bayan barinsa mulki a 2007. Ba shi da iko da kowace jiha a Najeriya.”
Ya kwatanta hakan da wasu ’yan siyasa, inda ya ce Asiwaju yana da tasiri a Legas, yayin da Nyesom Wike ke da iko a Jihar Ribas.
'Dan Atiku Abubakar ya koma APC
A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kan matakin ɗansa na shiga jam’iyyar APC daga PDP, lamarin da ya ja hankalin 'yan siyasa da sauran jama'a.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa sauya shekar ba shi ne abin da ya fi damunsa a yanzu ba, yayin da ya dage wajen ganin an kawo karshen gwamnatin APC mai ci a Najeriya a zaben 2027 mai zuwa.
Abubakar Atiku Abubakar wanda aka fi sani da Abba, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Alhamis, 15 ga Janairu, 2026, a harabar majalisar tarayya, inda ya goyi bayan Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

