APC Ta Yi Wa Atiku Shagube bayan Dansa Ya Ki Binsa zuwa ADC

APC Ta Yi Wa Atiku Shagube bayan Dansa Ya Ki Binsa zuwa ADC

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan matakin da dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dauka na kin bin mahaifinsa zuwa ADC
  • Ta bayyana cewa matakin na Abubakar Atiku Abubakar manuniya ce da ke nuna rashin amincin siyasar tsohon dan takarar shugaban kasar na Najeriya
  • Hakazalika, APC ta ragargaji Atiku Abubakar kan yadda ya yi kaurin suna wajen sauya sbeka daga wannan jam'iyya zuwa wancan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi magana kan matakin da Abubakar Atiku Abubakar ya dauka na shiga cikinta da marawa Shugaba Bola Tinubu baya.

APC ta bayyana matakin da ɗan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ɗauka na kin shiga jam’iyyar ADC a matsayin babban koma-baya ga amincin siyasar Atiku.

APC ta yi wa Atiku Abubakar shagube
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce kakakin APC a jihar Legas, Seye Oladejo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani da dansa ya sauya sheka zuwa APC, zai goyi bayan tazarcen Tinubu

Seye Oladejo ya mayar da martani kan rahoton sauya sheƙar ɗan na Atiku Abubakar zuwa jam'iyyar APC daga PDP.

Me APC ta ce kan sauya shekar dan Atiku?

A cewar Oladejo, jam’iyyar ta lura da matakin da Abubakar Atiku Abubakar ya dauka na barin abin da ya kira “tsarin ADC na karya” tare da komawa APC.

“Wannan aiki guda ɗaya ya faɗi abin da tarurrukan manema labarai dubu ba za su iya faɗa ba."
"Idan ɗan mutum ya yi watsi da hukuncin siyasar mahaifinsa, ya ki zaɓinsa, ya kuma rungumi wata hanya daban, ’yan Najeriya na da ’yancin tambayar wane karin hujja ake buƙata kan rashin amincin siyasa."
"Idan waɗanda ke zama mafi kusa da kai ba su gamsu da ra’ayinka na siyasa ba, ta yaya kake sa ran al’umma baki ɗaya su yarda?”

- Seye Oladejo

APC ta ragargaji Atiku

Oladejo ya kuma zargi Atiku Abubakar da rashin daidaito a akidar siyasa tsawon shekaru, inda ya bayyana tafiyarsa a siyasa a matsayin:

“Tafiya marar tabbas da ke cike da sauya jam’iyya sau da dama da tsananin sha’awar kujerar shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ya goyi bayan tazarcen Tinubu

“Daga PDP zuwa AC, daga nan ya koma PDP, sannan yanzu ADC, siyasarsa ba komai ba ce illa buri mai yawo daga jam’iyya zuwa jam’iyya yana neman wadda za ta sayar da ranta."

- Seye Oladejo

Dan Atiku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Abubakar Atiku Abubakar tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Ya ce matakin ɗan Atiku na shiga APC wata manuniya ce mai bayyana kin amincewa da tsarin siyasar da aka daina yayinta.

Seye Oladejo ya ce wannan mataki na nuni da goyon baya ga ayyukan mulkin APC da kuma Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Martanin Atiku kan shigar dansa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi martani kan matakin da dansa ya dauka na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa matakin da dan nasa ya dauka ba sabon abu ba ne a cikin tsarin dimokuradiyya inda kowa da 'yancin bin ra'ayinsa.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa ba ya tursasawa 'ya'yansa kuma matakin dan nasa na kashin kansa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng