Atiku Ya Yi Martani bayan Dansa Ya Sauya Sheka zuwa APC da Goyon bayan Tazarcen Tinubu
- Abubakar Atiku Abubakar wanda yake da ne a wajen tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Mahaifinsa Atiku Abubakar ya fito ya yi magana kan sauya shekar da ya yi tare da nuna goyon bayansa ga tazarcen Mai girma Bola Tinubu a zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa a tsari irin na dimokuradiyya, hakan ba sabon abu ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kan matakin da ɗaya daga cikin ’ya’yansa ya ɗauka na shiga jam’iyyar APC.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa sauya shekar ba ta daga cikin abin da ya fi damunsa a yanzu.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani rubuta da ya yi a shafinsa na X a daren ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.
Dan Atiku ya koma APC daga PDP
Legit Hausa ta ruwaito yadda ɗan Atiku, Abubakar Atiku Abubakar wanda aka fi sani da Abba, ya shiga jam’iyyar APC ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026 a harabar majalisar tarayya.
Abubakar Atiku Abubakar ya samu tarba daga wajen mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da manyan shugabannin APC daga shiyyar Arewa maso Gabas.
Da yake jawabi a wajen taron, Abba ya sanar da cikakken goyon bayansa ga APC, yana mai bayyana lokacin a matsayin abin tarihi kuma na kashin kai.
Haka kuma, ya umarci dukkan jagorori da mambobin kungiyar siyasar da ya kafa a 2022, wadda a baya aka sani da Haske Atiku Organisation, da su gaggauta shiga APC tare da mara wa ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu baya.
Wane martani Atiku ya yi?
Sai dai da yake mayar da martani, Atiku, wanda ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, ya ce matakin na ɗansa abu ne na kashin kansa.
“Matakin da ɗana, Abba Abubakar, ya ɗauka na shiga APC nasa ne na kashin kansa. A tsarin dimokuraɗiyya, irin wannan zaɓi ba sabon abu ba ne, kuma ba abin tayar da hankali ba ne, ko da kuwa siyasa da alaka ta jini sun haɗu."
“A matsayina na ɗan dimokuraɗiyya, ba na tilasta wa ’ya’yana a batun abin da suka yarda da shi, kuma tabbas ba zan tilasta wa ’yan Najeriya ba."
"Abin da ya fi damuna shi ne mummunan mulkin APC da tsananin wahalhalun tattalin arziki da zamantakewa da ta dora wa al’ummarmu.”
"Ina ci gaba da jajircewa wajen aiki tare da masu kishin kasa masu ra’ayi iri ɗaya domin dawo da ingantaccen mulki da kuma ba ’yan Najeriya wata sahihin zabin da zai kawo sauki, kwarin gwiwa da ci gaba.”
- Atiku Abubakar

Source: Twitter
Atiku ya magantu kan takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan batun janye takara a zabe shugaban kasa na shekarar 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya sha alwashin ba zai janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba da ke tafe.
Atiku ya kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya, ta hanyar rage karfin jam’iyyun adawa.
Asali: Legit.ng

