‘Annoba ne ga Jam’iyyu’: Tsohon Dan Takarar Gwamnan Kano Ya Faɗi Matsalar Kwankwaso
- Tsohon dan takarar gwamna a Kano, Ja’afar Sani Bello ya yi magana game da dambarwar siyasa da ke faruwa a jihar
- 'Dan siyasar ya ce tasirin siyasar Rabiu Kwankwaso ya ta’allaka ne kawai a Kano, yana mai cewa ba shi da karfin tasiri a matakin kasa
- Ja'afar Bello ya kuma jero manyan 'yan siyasa a Arewacin Najeriya da suke da tasiri a siyasar yankin gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Ja’afar Sani Bello, ya soki tsarin siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ja'afar Sani Bello ya yi watsi da karfin tasirin siyasar tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, yana mai cewa tasirinsa bai wuce jihar Kano ba.

Source: Facebook
Ja'afar Sani Bello ya dura kan Rabiu Kwankwaso

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta hango lam'a a kalaman Kwankwaso na tilasta wa masoyansa koma wa APC
Ja’afar Bello ya bayyana hakan ne a wani bidiyo yayin tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Daily Politics' na Trust TV da ta wallafa a Facebook a ranar Laraba 14 ga watan Janairun 2025.
Ya ce Kwankwaso bai daga cikin wadanda suke da tasiri matuka a siyasance a yankin Arewa inda ya jero guda uku amma babu sunan jagoran Kwankwasiyya a ciki.
'Dan siyasar ya ce duk jam’iyyar da Kwankwaso ya shiga za ta fuskanci matsaloli saboda rashin karfin jagoranci a matakin kasa da dalilai da dama na siyasa.
An jero 'yan siyasa da suka fi Kwankwaso
A cewarsa, Kwankwaso bai da irin farin jini a kasa idan aka kwatanta da manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai, wadanda duk suka shiga jam’iyyar ADC ba tare da wani sharadi ba.
Ya ce:
“Atiku ya shiga ADC ba tare da sharadi ba, haka Peter Obi da El-Rufai. Dukkansu suna da karfin tasiri a kasa fiye da Kwankwaso.”
'Yadda zaben 2023 ya raba gardama' - Ja'afar
Ya kara da cewa sakamakon zaben da ya gabata ya nuna karara cewa Kwankwaso ya dogara ne kacokan da Kano amma ba shi da wani tasiri a sauran jihohin Najeriya.
Ja'afar ya bayyana kuri'u da Kwankwaso da sauran manyan yan takara suka samu wanda ya tabbatar da gazawar jagoran siyasar Kwankwasiyya.
“Atiku ya samu kuri’u miliyan 7, Peter Obi ya samu miliyan 6, yayin da Kwankwaso ya samu kuri’u miliyan 1.14 kacal, kuma kashi 90 cikin 100 daga Kano ne.”
- Ja’afar Sani Bello
NNPP ta magantu kan juya kalaman Kwankwaso
An ji cewa jam'iyyar NNPP ta kuma musanta wani rahoto da ke yawo cewa Kwankwaso ya amince da shirin Gwamna Abba Yusuf na komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
NNPP ta zargi wasu mutane daga cikinta da Kwankwasiyya da yada labarin karya domin biyan bukatar kansu ta siyasa da kuma kara hura wutar rikicin a jihar.
Wannan martani na zuwa ne bayan an ruwaito cewa wai Kwankwaso ya marawa Abba baya ya koma APC wanda ke nuna ya janye neman tilasta shi ci gaba a NNPP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
