Tsohon Dan Majalisa Ya Yi Gaba, Ya Koma APC ana Batun Sauya Shekar Gwamna a Kano

Tsohon Dan Majalisa Ya Yi Gaba, Ya Koma APC ana Batun Sauya Shekar Gwamna a Kano

  • Tsohon Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Tsanyawa/Ghari, Hon. Sufiyanu Mohammed Harbau, yaha daruruwan 'yan NNPP zuwa APC
  • Hon. Sufiyanu Mohammed Harbau da ya samu tarbar Mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I. JIbrin ya ce bai taba yanke zumunci da APC ba
  • Da ya ke karbarsa, Sanata Barau ya yi alkawarin za a yi wa tsohon dan majalisan adalci da haɗin kai domin ci gaba a Kano ta yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sanata Barau I Jibrin ya sanar da karɓar tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Tsanyawa/Ghari, Hon. Sufiyanu Mohammed Harbau.

Hon. Sufiyanu Mohammed Harbau ya koma jam'iyya mai mulki ta APC a lokacin da ya kai masa ziyara a Majalisar Tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Wannan siyasar ba a zaƙalƙale mata:" Kwankwaso ya bi ta kan yaran Abba

Barau Jibrin ya karbi Harbau
Sanata Barau I Jibrin a yayin karban Harbau da mutanensa Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau I Jibrin ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da a wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ya karbi Hon. Harbau da daruruwan magoya bayansa.

Dalilin tsohon dan majalisae na komawa a APC

Hon. Sufiyanu Mohammed Harbau ya yayin taron, ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar NNPP ne domin komawa gidansa na siyasa wato APC.

Sanata Barau ya yi dadin sauya shekar Hon Harbau
Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

A cewarsa:

“Na dawo APC a yau tare da duk abokan aikina da magoya bayana. Ban taba barin gidana na siyasa ba. Ko lokacin da nake NNPP, mutanena sun zabe ka, Sanata Barau. Mun ci gaba da hulɗa tun lokacin da na bar APC, kuma yau na dawo gida tare da mutanena.”

Ya ƙara da cewa Sanata Barau ya yi ayyuka masu yawa ga al’ummomin Ghari da Tsanyawa tun kafin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

A kalamansa:

"Ka gina hanyoyi, ka tallafa wa al’ummomi, ka aiwatar da ayyuka da dama. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar shiga APC saboda kai."

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

APC: Barau zai hada kai da Harbau

Sanata Barau ya bayyana farin cikinsa kan dawowar Hon. Harbau, yana mai cewa ba kawai abokin siyasa ba ne, illa amini kuma wanda ya tsaya masa a lokutan ƙalubale.

Ya ce dangantakarsu ta dade tun shekaru masu yawa duk da bambancin jam’iyya, saboda burinsu ɗaya na ciyar da al’umma gaba.

Barau ya tabbatar wa Hon. Harbau da magoya bayansa cewa APC jam’iyya ce ta adalci da haɗin kai, kuma ba za a nuna bambanci ba.

Ya ce:

“Za a ɗauke ku daidai da sauran ‘ya’yan jam’iyya. Babu wariya, babu banbanci."

Haka kuma, ya jaddada goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa gwamnatin na aiki tukuru domin bunƙasa ƙasar nan.

Sanata Barau ya kuma sake jaddada kudirinsa na sauya fasalin Kano ta Arewa ta hanyar ayyuka da shirye-shiryen da suka shafi jama’a kai tsaye.

Kwankwaso ya kafa sharadin komawa APC

Kara karanta wannan

Da gaske Kwankwaso ya goyi bayan Abba Kabir zuwa APC? NNPP ta fayyace gaskiya

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a matakin ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana matsayinsa kan jita-jitar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Sanata Kwankwaso ya ce duk wani tunani ko shiri na shiga APC dole ne ya zo ne tare da cikakken tabbaci kan makomar jihar Kano da kuma jin daɗin magoya bayan jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso ya bayyana cewa duk wata tattaunawa kan APC dole ne ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da tafiya bisa turbar da jama’a suka zaba ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng