Abokin Takarar Kwankwaso Ya Fito Ya Yi Magana ana Batun Shirin Abba na Komawa APC
- Dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar NNPP a zaben 2025, Bishof Isaac Idahosa ya jaddada goyon bayansa ga Kwankwaso
- Babban limamim cocin ya bayyana Dr. Rabiu Kwankwaso a matsayin jagora amintacce, wanda ke tsayawa talakawan da aka yi watsi da su
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin alaka ta yi tsami tsakanin jagoran NNPP da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Manyan jiga-jigan NNPP na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da dambarwar da ke faruwa musamman bayan bullar rade-radin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma APC.
Duk da har yanzu, gwamnan na jihar Kano bai fito ya yi magana da bakinsa ba amma jita-jitar na ci gaba da kara karfi, kuma alamu na nuna alaka ta yi tsami tsakaninsa da Kwankwaso.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa, dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar NNPP a zaben 2023 kuma babban limamin coci a Najeriya, Bishof Isaac Idahosa ya fito ya yabi Kwankwaso a wannan lokaci.
Bishof Idahosa ya goyi bayan Kwankwaso
Limamin cocin, wanda shi ne abokin takarar Kwankwaso a zaben 2023, ya bayyana madugun Kwankwasiyya a matsayin jagora mai kaunar talakawa.
Bishof Idahosa, ya bayyana cewa akwai wani babban aiki na kasa da ke jiran sa, yayin da ya sake jaddada goyon bayansa ga jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba, Idahosa ya kwatanta Kwankwaso da matsayin jagora amintacce wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin jin dadin talakawan Jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
Idahosa ya yaba da nagartar Kwankwaso
A rahoton Vanguard, Idahosa ya bayyana cewa:
"Kwankwaso gwarzon kasa ne wanda a kowane lokaci yake nuna damuwarsa ga gajiyayyu. Jagora ne abin dogaro wanda ko da yaushe yake tsayawa tsayin daka ga talakawan da aka maida saniyar ware.
"Kuma ni dai na yi amannar cewa yana daya daga cikin mutanen da za su iya ciyar da Najeriya gaba."

Source: Facebook
Limamin coci ya ba mambobin NNPP shawara
Malamin cocin ya yi kira ga mambobin jam’iyyar NNPP a fadin kasar nan da su hada kai su mara wa Kwankwaso baya, inda ya kara cewa:
"Hidimar kasa ne ke kiran Kwankwaso. Ya riga ya biya bashin da talakawa ke binsa, kuma nan ba da jimawa ba za a ji wata babbar sanarwa a matsayin sakamakon ayyukan kwarai da ya shuka," in ji shi.
Ya kammala da kira ga mambobin NNPP da su kara kaimi wajen goyon bayan manufofin Kwankwaso, yana mai cewa kishin kasa da hangen nesa irin nasa ne kadai zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki.
Mataimakin gwamna ya bi Kwankwaso
A baya, kun ji cewa an hangi mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a gidan jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso.
Aminu Gwarzo ya nuna alamun bangaren da ya dauka ne a daidai lokacin da rade-radin ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC ke kara karfi.
Mataimakin gwamnan na daya daga cikin manyan na kusa da Kwankwaso, wadanda ake hasashen za su iya ci gaba da zama a NNPP maimakon tafiya APC tare da Abba.
Asali: Legit.ng

