Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Abba Kabir Ya Tona Asirin Ganduje

Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Fadi Yadda Abba Kabir Ya Tona Asirin Ganduje

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwa ta musamman yayin da ake rade-radin ficewar Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC bayan dawowarsa Kano
  • Tsohon gwamnan ya soki tilasta wa mambobin NNPP goyon bayan sauya sheka, amma ya yaba wa Abba kan yabon gwamnatinsa da fallasa gazawar gwamnatin baya
  • A cikin bayanin da ya yi, Sanata Rabiu Kwankwaso ya mika godiya ga matasan jihar Kano da suka shafe shekara da shekaru suna gwagwarmayar Kwankwasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan halin da siyasar Kano ke ciki bayan dawowarsa jihar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin ganawa da magoya bayansa a Kano, inda ya ce tun bayan dawowarsa, ‘yan siyasa da dama ke kiran waya suna tambayarsa game da rade-radin ficewar gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fusata game da yadda Abba Ke Tilasta wa Ciyamomin Kano Binsa APC

Abba Kabir Yusuf, Rabiu Kwankwaso, Abdullahi Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje tare da Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: All Progressive Congress|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A bidiyon da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya yaba wa Abba Kabir bisa caccakar gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Maganar Kwankwaso kan Abba, Ganduje

A bayanin da Rabiu Kwankwaso ya yi, ya yaba wa Abba Kabir Yusuf kan yadda ya fito da abubuwan da gwamnatinsa ta kawo na cigaba a Kano.

Kwankwaso ya ce:

“A nan nake godewa mai girma gwamna, musamman jiya da ya yabi gwamnatinmu, kuma ya tona asirin waccar gwamnati (Gwamnatin Ganduje) wacce ta dakile abubuwa da yawa a wannan jiha tamu, jihar Kano.”

Kwankwaso ya kuma yi godiya ta musamman ga matasan Kano da ke ci gaba da mara masa baya a gwagwarmayarsa ta siyasa. Ya ce yana alfahari da jajircewarsu, tare da yin addu’ar Allah ya ba su nasara a dukkan kokarinsu.

Tun da ake magana game da rade-radin sauya sheka da irin maganganun da Rabiu Kwankwaso ke yi, har yanzu Abba Kabir bai yi martani kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa ciyamomin Kano abin da za su yi a shirin Abba na shiga APC

Abin da Abba ya fada kan gwamnatin Ganduje

A wani taro na kaddamar da tallafin koyon sana’a a Kano, gwamna Abba Kabir Yusuf ya soki gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

A sakon da hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature ya wallafa a Facebook Abba ya ce a lokacin Ganduje, an rufe cibiyoyin koyon sana’o’i da aka kafa a zamanin Kwankwaso domin horas da matasa ba tare da wani dalili ba.

Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Gwamnan ya tunatar da cewa cibiyoyin sun taimaka wajen bai wa matasa kwarewa ta hannu domin bunkasa tattalin arziki, amma gwamnatin da ta gabata ta dakile shirin.

Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar farfado da cibiyoyin tare da bai wa masu kammala horo takardun shaidar kwarewa da kayan aiki da jarin farawa.

Rabiu Kwankwaso ya karbi 'yan Kwankwasiyya

A wani labarin, mun kawo muku cewa tun bayan fara rade-radin sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC Rabiu Kwankwaso ke karbar 'yan Kwankwasiyya a gidajensa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso na karbar matasa, mata da kungiyoyi ne domin jaddada goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya da ya ke jagoranta.

A 'yan kwanakin da suka wuce, Kwankwaso ya karbi mutane da dama a gidajensa da ke Kano da birnin tarayya Abuja, inda ya ke karfafa su kan jajircewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng