Komawar Abba zuwa APC Ta Kankama, Zai Haɗu da Ganduje da Jiga Jigan APC a Kano

Komawar Abba zuwa APC Ta Kankama, Zai Haɗu da Ganduje da Jiga Jigan APC a Kano

  • Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai gana da Abdullahi Ganduje domin share fagen sauya sheƙa zuwa APC
  • An ce taron zai haɗa manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da Sanata Barau Jibrin, domin kammala shirin sauya sheƙar gwamnan
  • Rahotanni sun nuna cewa an ƙara tsaro a Gidan Gwamnatin Kano sakamakon tunanin tashin hankali tsakanin yan Kwankwasiyya da wasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana sa ran Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai gana da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a yau.

Wannan haduwar na zuwa ne gabanin sauya sheƙarsa daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda ya rikita siyasar jihar Kano.

Abba Kabir zai gana da Ganduje a Kano
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Gwamna Abba Kabir. Hoto: All Progressives Congress, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Abba Kabir zai gana da Abdullahi Ganduje

Wannan bayani ya fito ne daga Muhammad Garba, babban sakatare ga Ganduje yayin wata tattaunawa a gidan rediyo, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa ciyamomin Kano abin da za su yi a shirin Abba na shiga APC

Garba ya ce taron zai buɗe share ga sauya sheƙar gwamnan a Kano, inda manyan shugabannin APC za su halarta domin cimma matsaya ta ƙarshe game da barin gwamnan NNPP.

Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, za su halarci taron.

'Zuwan Abba Kabir zai karfafa APC'

A cewarsa, sauya sheƙar gwamnan da magoya bayansa zai taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar ta fuskar rajistar mambobi.

Garba ya ce zuwan Abba Kabir zai ƙara ƙarfin APC wajen tunkarar zaɓe a faɗin ƙasar nan, ta hanyar gina sahihiyar alaka da samun bayanan mambobi.

Ya ƙara da cewa aikin rajistar APC zai ƙarfafa tasirin jam’iyyar, bisa dogon tarihin biyayya da tsari da take da shi a Kano.

An shirya tarbar Abba Kabir a APC
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Shawarar da aka ba 'ya 'yan jam'iyyar APC

An kuma shawarci mambobin jam’iyyar da su zauna lafiya tare da goyon bayan ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Tinubu.

Manufar na mai da hankali kan bunƙasa tattalin arziki da walwalar jama’a, inda aka jaddada cewa haɗin kai na siyasa yana da muhimmanci.

A halin da ake ciki, an ƙara tsaurara tsaro a Gidan Gwamnatin Kano saboda tashin hankalin siyasa da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

An jibge motocin sulke guda biyu da tankin ruwan zafi a bakin ƙofar Gidan Gwamnatin Jihar Kano domin tabbatar da zaman lafiya.

Haka kuma, an ga ƙarin jami’an tsaro masu makamai, musamman daga hukumar DSS, suna sintiri a harabar gidan gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarin tsaron na da alaƙa da rikicin da ke ƙaruwa tsakanin Kwankwasiyya da wasu ƙungiyoyin magoya bayan gwamna.

Sauya sheka: Kwankwaso ya shawarci ciyamomi

Mun ba ku labarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya ba ciyamomin Kano shawarar sanya hannu kan takardar goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu rike da mukamai sun shiga mawuyacin hali har da kwanciya a asibiti saboda rigimar.

Jagoran na NNPP ya jaddada cewa masoyansa na nan daram suna jiran zaben 2027 domin nuna karfin Kwankwasiyya a Kano da kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.