Abba da Kwankwaso: Nazari kan Abin da ke Jawo Rikici tsakanin Gwamnoni da Iyayen Gidansu

Abba da Kwankwaso: Nazari kan Abin da ke Jawo Rikici tsakanin Gwamnoni da Iyayen Gidansu

Kano, Nigeria - Siyasar Najeriya na ci gaba da daukar hankali musamman saboda yadda gwamnoni ke rabuwa da iyayen gidansu, wadanda suka taimaka masu wajen darewa kan mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wannan lamari na rikicin yara da iyayen gidansu yana nuna sauyin da aka samu saboda burin siyasa, harkokin cikin gida na jam’iyyu, da kuma ldabarun neman mulki a Najeriya.

Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, daya daga cikin misalai mafi girma da suka faru a baya-bayan nan shi ne rade-radin lalacewar alakar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.

Yadda Gwamma Abba ya taso a siyasa

Gwamna Abba ya girma a fagen siyasa ne a ƙarƙashin jagoranci da tallafin Kwankwaso, ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan siyasar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya.

Tasirin Kwankwaso shi ne babban makamin da ya taimaka wa Abba Gida-Gida wajen hawa matsayinsa na siyasa, musamman a lokacin zaɓen gwamna na shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya fadi yadda Abba zai buga rikici da Ganduje

Shekaru da dama, Abba da Kwankwaso sun nuna kusancinsu a idon jama’a, inda gwamnan ke yawan yabon mai gidan nasa tare da yin watsi da jita-jitar rashin jituwa.

Gwamna Abba ya taba fitowa fili ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya raba su ko ya raunana alakar siyasarsu, kamar yadda tashar Channles tv ta kawo.

Ana zargin Abba zai rabu da Kwankwaso

To sai dai abubuwan da ke faruwa a Kano sun haifar da rudani kan alakar manyan jiga-jigan biyu, duk da har yanzu Gwamna Abba bai fito ya tabbatar da lamarin a hukumance ba.

Amma alamu daga bangaren Kwankwaso da wasu kalamai da ya furta a baya-bayan nan, sun tabbatar da cewa akwai kanshin gaskiya a rade-radin da ake cewa za su raba gari.

A wannan rahoton, mun yi nazari kan karuwar rigima tsakanin iyayen gida da gwamnonin da suka kafa, tare da duba dalilan da ke jawo rashin jituwa a tsakaninsu duba da abin da ke faruwa a Kano

Tarihin fadan gwamnoni da iyayen gidansu

A tarihin siyasar Najeriya, rabuwar Abba da Kwankwaso, idan ta tabbata, ba ita ce ta farko ba tsakanin gwamna mai ci da ubangidansa.

Kara karanta wannan

An samu matsala a shirin ganawar gwamnan Kano da Tinubu kan batun komawa APC

Wadanda suka fi jan hankali shi ne rabuwar Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan ya tsaya masa ya ci zaben a 2015 da kuma ta Nasir El-Rufa'i da Gwamna Uba Sani na Kaduna.

Haka nan rigimar Ministan Abuja, Nyesom Wike sa magajinsa, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas na daya daga cikin rikicin da ya fi daukar hankali a siyasar Najeriya daga 2023 zuwa yau.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Abba Kabir Yusuf yama jagorantar taro a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Dalilan sabanin gwamnoni da ubangida

Duba abin dake faruwa a Kano tsakanin Abba da Kwankwaso, da wanda ya faru lokacin da Ganduje yake mulki, akwai abubuwa da dama da ke iya jawo sabanin ubangida da yaronsa.

1. Karfin iko a harkokin mulki

Daya daga cikin manyan dalilan ballewar gwamnoni daga iyayen gidansu shi ne, don su samu damar tafiyar da harkokin mulki yadda suke so ba tare da katsalandan ba.

Bayanai daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa wannan dalili na daya daga cikin abin da ke dab da raba gwamnan Kano da Kwankwaso.

A wani rahoto da This Day ta tattaro, majiyoyin sun ce Gwamna Abba na neman yadda zai dogara da kansa a siyasa, sannan kuma ya tafiyar da gwamnatin Kano ba tare da tasiirn kowa ba.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Kwankwaso ya fito ya yi magana ana batun shirin Abba na komawa APC

"Babbar matsalar ita ce Kwankwaso ya fara takaicin yadda Abba ya fara ja da baya, ya rage masa biyayya, a tunaninsa, duk abin da gwamnati za ta yi sai an kai masa ya amince tukunna," in ji wata majiya.

Sun kuma yi ikirarin cewa Gwamna Abba ya fara damuwa da karfin ikon Kwankwaso ne a lokacin nadin shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano.

An ce mai girma gwamna ya so Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya ci gaba da rike mukamin amma Kwankwaso ya dage dole sai an nada na yanzu.

Yusuf Yusuf, wani dan gidan Ganduje a siyasar Kano ya shaidawa wakilin mu cewa batun tafiyar da mulki musamman nade-nade ke sa yan siyasa na barin Kwankwaso.

"Bari na tuna maka wani abu, farkon lokacin da maigida (Ganduje) ya fara samun matsala da Kwankwaso shi ne batun nade-nade. Shi so yake duk abin da ya ce a bi, shi kuma maigida yana da na shi lissafin."
"Tunda aka kafa wannan gwamnatin, na san idan Kwankwaso ya kyale Abba ya yi mulki to za su ci gaba da zama a inuwa daya, amma matukar ya ce zai juya shi, na san duk daren dadewa za a zo nan," in ji shi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa ciyamomin Kano abin da za su yi a shirin Abba na shiga APC

2. Rikicin cikin gida a jam'iyya

Rikicin jam'iyya na taka rawa wajen raba gwamnoni da wadanda suka taimaka masu suka dare kan mulki, musamman kan butun wanda zai rika jagorantar al'amuran jam'iyya.

NNPP na daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa da ke fama da rikicin cikin gida, wanda ya kai ga darewarta gida biyu, tsagin Kwankwaso da kuma tsagin Major Agbo, in ji The Nation.

Gwamna Abba ya duba wannan matsala wajen fara tunanin barin jam'iyya saboda gudun kar abin da ya faru da APC a jihar Zamfara bayan zaben 2019 ya faru da jam'iyyar NNPP a Kano.

Gwamna Abba da Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da ubangidansa na siyasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

3. Burin siyasa

Wani abu da ke kara kawo tangarda a tafiyar siyasar ubangida a Najeriya shi ne burin siyasa, ko neman mulki.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka rabu da iyayen gidansu, sun yi haka ne da tunanin komawa inda za su samu damar neman tazarce a kan mulki.

Gwamna Abba na daga cikin wadanda ake ganin wannan dalili ya yi tasiri a kansa, domin wasu majiyoyi sun yi zargin cewa Kwankwaso na shirin karbe tikitin takara daga hannunsa a 2027, in ji rahoton Bussiness Day.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

Ra'ayin wani 'dan Kwankwasiyya

Wani 'dan Kwankwasiyya a Kano, Malam Sanusi Sulaiman ya shaidawa Legit Hausa cewa karuwar abin da suke kira da 'cin amana' a siyasar Kano na nuna akwai wani abu a kasa.

Sanusi, wanda ya tabbatar da cewa zai sake zaben Abba a duk jam'iyyar da ya koma, ya ce suna kaunar Kwankwaso, amma ya kamata ya gyara wasu abubuwan da ake zarginsa.

Ya ce:

"Wani lokacin idan magana ta yi yawa ta iya zama gaskiya, Kwankwaso mutumin kirki ne, amma ya kamata ya rika barin duk wanda ya taimaka ya samu mulki, domin ya sauke nauyin da ke kansa.
"Yawan katsalandan musamman abin da ya shafi kujerar gwamna, dole ya haifar da irin wannan, ni dai fata na, Abba da Kwankwaso su ci gaba da zama a inuwa daya, idan ma dole ne tafiya APC, su tafi tare.'

Dalilan jinkirin sauya shekar Abba

A wani rahoton, kun ji cewa an fara jin dalilan da suka jawo jinkirinsauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kara kaimi wajen shawo kan jama'a, Abba na shirin shiga APC

Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Abba ya jinkirta shiga APC ne domin kammala tuntubar wasu muhimman masu ruwa da tsaki.

Daga cikin dalilai uku da aka tattaro, akwai sharadin da Shugaba Tinubu ya gindaya wa Abba na zama da masu ruwa da tsakin APC da NNPP a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262