2027: Waye Tinubu Zai Zaba tsakanin Wike da Fubara? Tsohon Gwamna Ya Magantu

2027: Waye Tinubu Zai Zaba tsakanin Wike da Fubara? Tsohon Gwamna Ya Magantu

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya yi magana game da rikicin siyasar jihar Rivers a ranar 12 ga watan Janairun 2026
  • Ayo Fayose ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai sadaukar da Ministan Abuja, Nyesom Wike, domin Gwamna Siminalayi Fubara ba
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Wike ya fi Fubara muhimmanci a siyasa ga Tinubu, saboda rawar da yake takawa da nasarorin da APC ke samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya fadi wanda yake ganin Shugaba Bola Tinubu zai karkata gare shi a rikicin siyasar Rivers.

Fayose ya ce Tinubu ba zai taba sadaukar da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ba domin Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.

An fadi wanda Tinubu zai fi so tsakanin Wike da Fubara
Ministan Abuja, Nyesom Wike, Bola Tinubu da Siminalayi Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

'Wanda ya fi muhimmanci tsakanin Wike da Fubara'

Kara karanta wannan

Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja

Fayose ya fadi hakan ne yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, inda ya yi tsokaci kan rikicin siyasar Rivers.

Ya ce rikicin ya samo asali ne daga takaddamar neman iko tsakanin Gwamna Fubara da magabacinsa, Wike, wanda ke ci gaba da haddasa rashin kwanciyar hankali.

A cewarsa, Nyesom Wike ya fi Fubara muhimmanci a fagen siyasa ga Shugaba Tinubu, don haka babu dalilin da zai sa shugaban ya yi watsi da shi.

Fayose ya ce:

“Asiwajun da na sani ba zai kawar da Wike saboda Fubara ba, domin Wike ya fito daga Rivers ya ba Tinubu cikakken goyon baya.”

Ayo Fayose ya yabawa kokarin Wike a Abuja

Fayose ya kara da cewa Wike na yin aiki tukuru a Abuja, inda ya ce APC ta samu nasarori da dama sakamakon tasirin Wike a siyasance.

Ya kara da cewa:

“Wike yana aiki a Abuja, yana aiki tukuru, ba mu taɓa samun irin wannan ci gaba a Abuja ba; ko makaho ma ba zai iya musanta hakan ba.

Kara karanta wannan

A karon farko, Fubara ya yi magana ga al'ummar Rivers game da shirin tsige shi

“APC ta lashe ƙananan hukumomi a Jihar Rivers ne saboda gudunmawar Wike. Zaɓen ƙananan hukumomin da ke tafe a Abuja ma APC za ta yi nasara. To, me kuma Shugaban Ƙasa zai ƙara nema daga Wike?”
Fayose ya fadi muhimmancin Wike ga Tinubu
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose. Hoto: Ayodele Fayose.
Source: Twitter

Fayose ya caccaki halayen Gwamna Fubara

Dangane da kokarin Fubara na neman sa hannun Shugaban kasa, Fayose ya ce hakan alama ce ta bukatar taimako da rashin nuna tawali’u.

Fayose ya kuma musanta zargin cewa Tinubu ne ke haddasa rikicin PDP, yana mai cewa jam’iyyar ce ta jefa kanta cikin matsala, cewar Vanguard.

Ya ce PDP ta lalace ne sakamakon rikicin cikin gida, yana mai kwatanta jam’iyyar da gida da ya rabu wanda zai yi wahala a shawo kan matsalar da ke ciki.

Kungiya ta roki Tinubu ya kori Wike

Mun ba ku labarin cewa Kungiyar NADECO USA ta tura bukata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu game da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

'Yan NADECO na reshen kasar Amurka sun roki shugaban da ya dauki matakin gaggawa kan Wike domin kawo ƙarshen rikicin siyasa a Jihar Rivers.

NADECO USA ta ce Wike ne tushen rikicin Rivers, tana gargadin cewa idan shugaban ƙasa bai ɗauki mataki ba, rikicin zai ƙara muni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.