Tambuwal Ya Gano Babbar Matsalar da Ta Addabi Bangaren Zabe a Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi maganganu kan tsarin zabe a Najeriya
- Aminu Tambuwal ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da kura-kurai wajen gudanar da zabubbuka a kasar nan
- Tsohon shugaban majalisar wakilai ya kuma koka da cewa jam'iyyun siyasa ba su da wata tsayayyar akida da suke amfani da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon shugaban majalisar wakilai ta kasa, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana kan zabe a Najeriya.
Tambuwal ya ce zabe a Najeriya ba ya dogara kacokan da ra’ayin masu kada kuri’a, yana mai danganta hakan da kura-kurai da matsaloli a tsarin gudanar da zabe.

Source: Facebook
Tambuwal ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise Tv.

Kara karanta wannan
"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu
Me Aminu Tambuwal ya ce kan zabe a Najeriya?
Ya bayyana cewa duk da cewa ’yan Najeriya na fita suna kada kuri’a, sakamakon zabe na gaskiya ya kan lalace ne a matakin tattara sakamako.
“Zabe ba ya kammaluwa bisa cikakken ra’ayin masu kada kuri’a. Zan iya fadar hakan ba tare da sassauta harshe ba."
"Mun sani cewa sau da yawa, a matakin tattara sakamako ko a rumfunan zabe, ko a matakin gunduma, ko karamar hukuma, ko jiha, ko ma kasa, akwai abubuwan da ke faruwa da ke sauya ainihin abin da masu kada kuri’a suka zaba.”
- Aminu Waziri Tambuwal
Wace matsala Tambuwal ya gano?
A cewarsa, ’yan siyasa na yawan amfani da gibi da ke cikin tsarin zabe domin murde sakamako, musamman a matakan tattarawa da kuma isar da sakamakon kuri’u.
Ya kuma dora wani bangare na matsalar kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda ya ce wasu jami’an hukumar na yin abin da ke lalata sahihancin zabe.
Sai dai duk da haka, tsohon gwamnan ya nuna cikakken goyon bayansa ga duk wani gyara da zai inganta tsarin zabe a Najeriya, ciki har da aika sakamakon zabe ta hanyar na'ura.
“Ina goyon bayan duk wani gyara da zai inganta tsarin zabe a Najeriya, ciki har da aika sakamakon zabe ta na’ura."
- Aminu Waziri Tambuwal

Source: Twitter
Kalaman Tambuwal kan jam'iyyun siyasa
Dangane da tushen akida na jam’iyyun siyasa a Najeriya, Tambuwal ya ce yawancin jam’iyyun ba su da tsayayyar akida, yana mai cewa jam’iyyun kawai hanyoyi ne da ake amfani da su don cimma buri na siyasa.
“Idan maganar akida ce, me ya sa Shugaba Muhammadu Buhari yake cikin APC tare da wasu mutane da ke cikinta? Ba na son ambaton suna, amma idan aka kalli yadda ake kallon Buhari a wancan lokaci, me yake yi tare da wasu ’yan siyasa?”
- Aminu Waziri Tambuwal
Sanata Tambuwal ya fadi hanyar kifar da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.
Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa ya tsunduma gaba ɗaya cikin kokarin da shugabannin adawa ke yi domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan ya ce Tinubu ba zai kai labari ba idan manyan shugabannin 'yan adawa kamar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rabiu Kwankwaso suka hada kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

