Baffa Babba 'Dan Agundi: Yadda Ganduje Ya So Kwankwaso Ya Jawo Abba zuwa APC

Baffa Babba 'Dan Agundi: Yadda Ganduje Ya So Kwankwaso Ya Jawo Abba zuwa APC

  • Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ɓacin ransa kan kalaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi a kansa
  • Duk da haka, Ganduje ya bayyana cewa APC na maraba da lale da yiwuwar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf ikon jam’iyya mai mulki a sama
  • Makusancin tsohon Gwamnan, Alhaji Baffa Babba 'Dan Agundi ne ya tabbatar da haka ana zaman jiran sauya shaƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano –Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wasu kalamai da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a kansa.

Tsohon Gwamnan na Kano ya bayyana kalaman da cewa ba su dace ba, kuma masu tayar da hankali ne a yayin da maganar sauya sheƙa Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kwari.

Kara karanta wannan

"Bai yi butulci ba": Kwamishina a Kano ya wanke Abba daga zargin juya wa Kwankwaso baya

Ganduje na son a dinke baraka da Kwankwaso
Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Hagu), Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso (Dama) Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan bayani ya fito ne daga makusancin Ganduje, Dr. Baffa Babba Dan’agundi, yayin da yake zantawa da manema labarai kuma aka wallafa a shafin Facebook na DC Hausa.

Kalaman Rabiu Kwankwaso sun damu Abdullahi Ganduje

A cewar Baffa Babba 'Dan Agundi, Ganduje ne da kansa ya bayyana masa yadda kalaman suka dame shi matuƙa, kuma bai ji dadinsu ba.

Ya ce:

“Dr. Ganduje ya shaida min cewa bai ji daɗi ko kaɗan da kalaman da Sanata Kwankwaso ya yi a kansa ba."

'Dan Agundi ya bayyana cewa Ganduje ya zargi Sanata Kwankwaso da kiransa da suna makiya a gaban magoya bayansa.

Ganduje ya ce shi da Kwankwaso sun zama dattawa a siyasa
Tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Ya ce hakan ya faru ne a lokacin da Kwankwaso ke zargin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da shirin ƙwace iko da wasu hukumomin gwamnati domin amfani da su kan abokan hamayyarsa na siyasa.

Ya ce:

“Ganduje ya bayyana min cewa irin waɗannan kalamai ba su dace ba, musamman a wannan lokaci da Jihar Kano ke buƙatar haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba na bai ɗaya.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: 'Dan Kwankwaso ya zabi wanda zai bi tsakanin mahaifinsa da Gwamna Abba

APC na maraba da Gwamna Abba Gida Gida

Ya ƙara da cewa Ganduje ya yi imanin cewa yiwuwar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC ya kamata ta zama dama ta sulhu da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar, ba sabani da ƙarin rikici ba.

Ya ce:

“A fahimtar Ganduje, dawowar Gwamnan Kano APC ya kamata ta zama wata hanya da za a haɗu, a manta da banbance-banbance, a mayar da hankali kan ciyar da Kano gaba."

Dr. Ganduje ya kuma jaddada cewa, la’akari da shekarunsu da gogewarsu a siyasa, shi da Sanata Kwankwaso ya kamata su rika taka rawar dattawan ƙasa, maimakon ci gaba da rikicin siyasa.

Ya ce:

“Ya yi imanin babu dalilin ci gaba da saɓani, domin dukkanninsu sun kai matakin da ba su da wata babbar buƙata ta siyasa, tunda sun kammala iyakar wa’adin rike muƙaman zaɓe."

Da yake magana kan rahoton dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf APC, Dan’agundi ya bayyana hakan a matsayin abin farin ciki da ƙarfafawa ga jam’iyyar APC a Kano.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

Ya ƙara da cewa shirye-shiryen tarbar Gwamnan a hukumance sun yi nisa, ya kuma yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da haɗin kai a Kano, tare da fatan dawowar Gwamna Abba APC za ta haifar da ci gaba mai ɗorewa.

An jibge jami'an tsaro a gidan gwamnati Kano

A baya, kun ji rahotanni sun tabbatar da cewa an ƙara tsaurara matakan tsaro a Fadar Gwamnatin Jihar Kano a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.

An ga ƙarin jami’an tsaro a harabar fadar, motocin yaki da kara tsaurara tsaro, abin da ya ja hankalin mazauna Kano tare da manema labarai a jihar.

Ana ganin matakin ya biyo bayan rade-radin da ke yawo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng