Fubara: Majalisar Dokokin Ribas Ta Ja Kunnen Masu Yunkurin Hana Ta Tsige Gwamna

Fubara: Majalisar Dokokin Ribas Ta Ja Kunnen Masu Yunkurin Hana Ta Tsige Gwamna

  • Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta bayyana cewa ana yunkurin ɓoye na hana shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa
  • Majalisar ta yi zargin cewa wasu da neman umarnin kotu daga kotunan jihar da ba na rukunin Fatakwal ba domin hana ta tsige Gwamna
  • Ta ce kundin tsarin mulki ya haramta kotuna shiga harkar tsige shugabannin da aka zaɓa, saboda haka wannan yunkuri baya bisa doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers – Majalisar dokokin jihar Ribas ta bayyana damuwa kan abin da ta kira yunkurin na wasu mutane da ba a bayyana sunayensu ba na hana tsige Gwamna.

Ta ce mutanen na ƙoƙarin amfani da wasu kotunan babban birnin jihar Rivers da ke wajen rukunin shari’a na Fatakwal domin karya ko raunana shirin tsige Gwamna da Mataimakiyarsa.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Majalisa ta yi zargin ana son Hana ta tsige Gwamna
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Janairu, 2026, da Shugaban kwamitin gada labarai, Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar, Hon. Dr. Enemi Alabo George ya fitar.

Majalisa: Ana son hana tsige Gwamnan Ribas

Daily Post ta ruwaito majalisa ta ce ta samu sahihan bayanai cewa wasu mutane na neman umarnin kotu domin hana Majalisar aiwatar da ayyukanta na kundin tsarin mulki ta haramtacciyar hanya.

’Yan Majalisar sun yi gargaɗi cewa duk wani mataki irin haka, idan aka aiwatar da shi, zai zama keta wa da rushe Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya.

Sun jaddada cewa irin wannan yunkuri ya sauka daga kan turbar doka da oda ba, kuma zai iya haifar da barazana ga tsarin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Shugaban ƙaramar hukuma a Binuwai ya nemi ɗauki kan karuwar ƴan ta'adda

Majalisar ta kuma ambaci Sashe na 272(3) da 188(10) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 waɗanda ke hana kotuna karɓar shari’o’in da suka shafi tsarin tsige shugabanni.

Sanarwar ta ce:

“Waɗannan mutane sun san hukunce-hukuncen shari’a da suka gabata a kan wannan batu, musamman kwanan nan a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan wani lamari makamancin haka da ya shafi umarnin ex parte da Kotun Babban Birnin Jihar Rivers ta bayar, wanda ya saba wa Sashe na 272(3) na kundin tsarin mulki. Kalma ɗaya ta isa ga mai hikima.”

Ta ƙara da cewa:

“Saboda haka, da izinin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas ina kira ga duk waɗanda abin ya shafa da su nuna haƙuri, su guji duk wani aiki da zai sabawa kundin tsarin mulki da bin doka."

Majalisa ta nace da shirin tsige Gwamna

Sanarwar ta tunatar da jama’a hukunce-hukuncen Kotun Ɗaukaka Ƙara na baya-bayan nan, waɗanda suka soke irin waɗannan umarni da aka bayar a baya. A cewar Majalisar, dukkanin masu riƙe da muƙamai da ake shirin tsige wa sun karbi sanarwar zargin manyan laifuffuka yadda ya dace.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Ta ƙara da cewa kuma ana sa ran za su mayar da martani bisa doka, maimakon yin abin da Majalisar ta kira “hanyoyin ɓoye-ɓoye” domin hana bin ƙa’ida.

Majalisa ta ce shirin tsige Gwamna na nan daram
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ke fuskantar tsige wa a Majalisa Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Majalisar Dokokin Jihar Rivers, da amincewar Shugabanta, Rt/ Hon. Martin Chike Amaewhule, ta yi kira ga kowa da kowa da ya mutunta doka da oda.

Ta sake jaddada jajircewarta ga kundin tsarin mulki da dimokuraɗiyya, tana mai cewa ba za ta bari yunkurin ɓata suna ko tsoratar da ’ya’yanta ya karkatar da ita daga aikinta ba.

'Yan majalisa za su tsige Gwamnan Ribas

A baya, kun ji Majalisar dokokin Ribas ta ƙaddamar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Oduh, lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin siyasar jihar.

An ɗauki wannan mataki ne a yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisa, Rt. Hon. Martins Chike Amaewhule.

A yayin zaman, an karanta takardar zargin da ke ƙunshe da laifuffukan da ake tuhumar gwamnan da aikatawa a kan kujerarsa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng