2027: NNPP Ta Tsayar da Magana kan ba Kwankwaso Takara, Ta Gargadi Masu Son a Yi Haɗaka

2027: NNPP Ta Tsayar da Magana kan ba Kwankwaso Takara, Ta Gargadi Masu Son a Yi Haɗaka

  • Jam'iyyar adawa ta NNPP ta ce Rabiu Musa Kwankwaso ba zai samu tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2027 ba
  • Jam’iyyar ta bayyana cewa har yanzu, ba a warware rrikicin da ke tsakaninta da tafiyar siyasar Kwankwasiyya ba
  • NNPP ta ce tikitin 2027 a buɗe yake ga dukkanin ƴaƴanta na hakika, har ma ta ja kunnen masu son haɗaka da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sakataren ƙasa na jam’iyyar NNPP, Ogini Olaposi, ya yi bayani game da makomar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A cikin wata sanarwar da ya fitar a jihar Legas a ranar Lahadi, Olaposi ya bayyana cewa Kwankwaso ba zai samu damar tsayawa takara a ƙarƙashin tutar NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya yi hasashen Atiku zai yi amfani da kuɗi don ruguza ADC

NNPP ta ce har yanzu ba ta warware matsalolin da ke tsakaninta da Kwankwasiyya ba
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana magana da ƴan jarida Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Olaposi ya jaddada cewa za a bayar da tikitin shugaban ƙasa na NNPP a 2027 ga ƴan jam’iyyar na gaskiya da suka cika sharudda.

Kwankwaso ya samu matsala da NNPP

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa NNPP ta ce Kwankwaso, wanda ya tsaya takara da tutar NNPP a babban zaɓen 2023, ya rasa damar sake neman tikitin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa wannan lamari ya biyo bayan rikice-rikicen da ba a warware ba tsakanin NNPP da ɗarikar siyasar Kwankwasiyya da Kwankwaso ke jagoranta.

Sakataren jam’iyyar ya ƙara da cewa NNPP ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da Kwankwasiyya a shekarar 2022, amma ya ce yarjejeniyar ta zo ƙarshe bayan kammala babban zaɓen 2023.

Ya zargi wasu ƴan Kwankwasiyya da aikata ayyukan cin amanar jam’iyya bayan zaɓen shugaban ƙasa, lamarin da ya ce ya kai ga korar manyan jagororinsu.

Ya bayyana cewa wadanda aka kora sun hada da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima da wasu daga cikin mabiyansu, wanda har yanzu ba a janye hukuncin korar ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa APC ke da kwarin guiwar samun nasara a zaben 2027'

Tikitin 2027 a buɗe yake ga kowa – NNPP

Olaposi ya bayyana cewa sabanin yadda aka yi a 2023, inda aka ba wa Kwankwaso tikiti kai-tsaye, jam’iyyar NNPP ta ɗauki tsarin ba kowane halattaccen dan jam'iyya damar ya baza komawarsa.

Ya ce:

“Tikitin NNPP na 2027 a buɗe yake ga duk yan jam’iyya, ba kamar a 2023 ba da aka bai wa Kwankwaso shi kaɗai.”
NNPP ta ce Kwankwaso ba zai samu tikitin takara a 2027 ba
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa jam’iyyar na fara ganin masu sha’awar neman takara daga cikin gida da kuma ƙasashen waje, kuma duka za su samu damar.

Olaposi ya ce:

“Tuni muna da masu sha’awar neman tikitin shugaban ƙasa, ciki har da biyu daga ‘yan NNPP mazauna ƙasashen waje, kuma muna maraba da ƙarin masu sha’awa har da haɗin gwiwa."

Olaposi ya kuma ce a shirye NNPP take ta yi haɗin gwiwa da wasu jam’iyyun siyasa masu ra’ayi iri ɗaya a zaɓen 2027.

Da yake mayar da martani kan maganganun da aka jingina wa Kwankwaso kan yiwuwar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, Olaposi ya ce hakan abin dariya ne.

Kara karanta wannan

ADC na shirin hadaka da PDP da NNPP domin kifar da Tinubu a 2027

A cewarsa:

“Abin dariya ne Kwankwaso ya ce idan zai koma wata jam’iyya, har da APC, dole su ba shi tikitin shugaban ƙasa.”

Ya yi iƙirarin cewa Kwankwaso ba shi da karɓuwa a faɗin ƙasa kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ƙarfinsa a Kano ma ya ragu.

Olaposi ya gargaɗi jam’iyyun da ke neman haɗin gwiwa da NNPP su tattauna ne kawai da sahihin shugabancin jam’iyyar da kotu ta amince da ita.

Kwankwaso ya tabo batun sauya sheƙar Abba

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya sake tabo batun rikicin sauya sheƙar Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, inda ya ce shi ne zai yi dariya a ƙarshe.

Kwankwaso ya fadi hakan ne yayin da ya ke karɓar ziyara daga masu goyon bayansa a gidansa da ke Kano, inda ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da nuna biyayya ga Kwankwasiyya.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf — wanda aka zaɓa a ƙarƙashin tutar NNPP a 2023 — ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng