A karon Farko, Fubara Ya Yi Magana ga Al'ummar Rivers game da Shirin Tsige Shi
- Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da majalisar dokoki ke ci gaba da yunkurin tsige shi daga mulki
- Fubara ya ce shiru da yake yi da gangan ne, saboda ya dogara da kuma mika imaninsa ga Allah
- Majalisar Rivers ta sake fara yunkurin tsige Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, tana zarginsu da rashin da’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi martani a karon farko kan dambarwar siyasar jihar Rivers.
Fubara ya bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu dangane da yunkurin tsige shi da majalisar dokokin jihar ta fara.

Source: Facebook
Kalaman Fubara bayan shirin tsige shi
Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin wani taron ibada na coci da aka gudanar domin tunawa da Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara
Fubara ya tabbatar wa jama’a cewa komai zai daidaita, yana mai nuna kwarin gwiwa duk da matsin lambar siyasa da ke tattare da yunkurin tsige shi.
Ya bayyana cewa shiru da yake yi kan wasu abubuwan da ke faruwa da gangan ne, yana mai cewa yana samun karfi ne daga dogaronsa ga Allah.
Gwamnan ya tuna da kalamansa a liyafar sabuwar shekara da aka gudanar a fadar gwamnati, inda ya ce “karnuka kan yi kuka idan ba su fahimta ba.”
Bayan kammala jawabin nasa, Fubara ya gayyaci mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, wadda tun da farko ta karanta darasi na farko a cocin.

Source: Instagram
Mataimakiyar Fubara ta yi magana
A jawabinta, Mataimakiyar Gwamna Ngozi Odu ta gode wa mahalarta taron bisa halartar su hidimar ibadar.
Ta bukaci kowa da kowa ya kiyaye halaye nagari, kamar yadda babban limamin cocin Anglican, Archbishop Blessing Eyinda, ya jaddada a hudubarsa.
Odu ta ce duk wani aiki da mutum ya aikata, tabbas za a tuna da shi a wani lokaci, don haka ya dace mutane su kasance masu tsoron Allah.
Ta kuma roki al’umma da su ci gaba da yi wa gwamnatin addu’a, tana mai bayyana addu’a a matsayin ginshikin da ke rike da mulki, cewar rahoton Punch.
A makon jiya ne, Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara yunkurin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa bisa zargin rashin da’a mai tsanani.
‘Yan majalisar sun kuma zargi gwamnan da kashe kudaden gwamnati ba tare da samun amincewar majalisar dokoki ba.
Wannan dai shi ne karo na biyu da majalisar ke kokarin tsige Fubara tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
An gargadi Fubara kan rigimar Fubara
Kun ji cewa Ayodele Fayose ya yi ikirarin cewa babu abin da zai ceci Gwamna Similayi Fubara daga rikicin jihar Ribas sai addu'o'i da azumi.
Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya tuna tattaunawar da ya yi da Wike lokacin da ya halarci bikin rantsar da Simi Fubara a 2023.
Kalaman Fayose na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Fubara da mataimakiyarsa.
Asali: Legit.ng
