Ana Jita Jitar Barin Abba NNPP, Ganduje Ya Dawo Najeriya, Zai Bazama Harkar Siyasa
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya daga hutun da ya yi a Dubai a kasar UAE
- Ganduje ya isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos kafin ya wuce Abuja domin ganawa da manyan jiga-jigan APC
- Tsohon gwamnan Kano zai shiga tattaunawar siyasa yayin da Abba Kabir ke shirin barin NNPP zuwa jam’iyyar APC mai adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya bayan shafe makonni yana hutawa a Dubai.
Ganduje ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos da misalin karfe 4:30 na yammacin Asabar 10 ga watan Janairun 2026.

Source: Facebook
Ganduje ya dawo Najeriya bayan hutu a Dubai
Hakan na cikin wata sanarwa daga shugaban ma’aikatansa, Malam Muhammad Garba ya fitar, cewar Vanguard.
Bayan isowarsa Lagos, ana sa ran Ganduje zai wuce Abuja daga baya domin ci gaba da shirye-shiryen siyasa da tattaunawa da jiga-jigan APC yayin da ake zargin Abba Kabir zai koma APC.
Bayan dawowarsa kasar, tsohon shugaban APC zai fara shawarwari da tarurruka da masu ruwa da tsaki kan halin siyasar jihar Kano.
Sanarwar ta ce:
“Bayan dawowarsa, ana sa ran tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa zai fara tuntubar abokan siyasa da tarurruka da masu ruwa da tsaki, domin tattauna sababbin sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano.
“Waɗannan ganawa, na da nufin nazartar yanayin siyasar da ke sauyawa tare da yin shawarwari da shugabannin jam’iyya da manyan masu ruwa da tsaki."

Source: Facebook
Ganawar da ake sa ran Ganduje zai yi
Wadannan ganawa za su hada da shugabannin jam’iyya da manyan masu tasiri, domin tantance sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jihar Kano.
Garba ya ce shawarwarin za su karfafa tattaunawa da hadin kai a jam’iyyar APC a Kano, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Ana sa ran Ganduje zai shiga shirin rajistar mambobin APC ta intanet, wanda aka kaddamar a lokacin shugabancinsa a matsayin shugaban jam’iyyar kasa.

Kara karanta wannan
Boye boye ya kare, majalisar Kano ta yi magana kan shirin Gwamna Abba na komawa APC
Sanarwar ta bayyana cewa Abdullahi Ganduje na da kudurin karfafa tsarin jam’iyyar APC da kuma tallafa wa dimokuradiyya ta hanyar ci gaba da tuntuba da hadin kai.
“Tsohon gwamnan ya ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa tsarin jam’iyya da kuma inganta tattaunawa mai haɗa kowa da kowa, domin tallafa wa ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin APC, musamman a Jihar Kano.”
- Cewar Garba
Ganduje ya taya Abba murnar cika shekaru 63
An ji cewa manyan 'yan siyasa sun taya Abba Kabir murna na cikarsa shekara 63 a duniya wanda ya yi masa addu'o'i na musamman da fatan alheri.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya aike da saƙonni masu ma’ana, abin da ya tayar da rade-radi kan siyasa.
Hakan na zuwa ne yayin da ake rade radin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC daga NNPP mai mulki a jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
