Tsohon Gwamna, Sanata Dickson Ya Koma Jam'iyyar Hadaka, ADC? Gaskiya Ta Fito

Tsohon Gwamna, Sanata Dickson Ya Koma Jam'iyyar Hadaka, ADC? Gaskiya Ta Fito

  • Tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa ADC
  • Dickson, sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce ya dauke kafa daga harkokin siyasa ne saboda jimamin rasuwar mataimakin gwamna
  • Ya ce bayan kammala zaman makoki, zai zauna da abokai da makusantansa kafin yanke kowane irin mataki a siyasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa, Nigeria - Sanatan Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya musanta rahotannin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar hadaka, ADC.

Sanata Dickson, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, ya ce har yanzu shi cikakken mamba ne na PDP, kuma ba zai ɗauki wani mataki na siyasa ba sai ya yi shawarwari.

Sanata Dickson.
Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Seriake Dickson Hoto: Seriake Dickson
Source: Facebook

Premium Times ta ruwaito cewa sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ajiri Daniels, ya fitar a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Shugaban kwamitin yakin zaben Uba Sani ya rabu da gwamna ya bi El Rufai zuwa ADC

Sanata Dickson na daga cikin fitattun ’yan adawa masu tashi suna magana sosai a Majalisar Dattawan Najeriya.

Ana jita-jitar Sanata Dickson ya koma ADC

A lokuta da dama, ya sha fitowa fili ya ƙalubalanci wasu daga cikin manufofin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

A ’yan kwanakin nan, rahotanni sun yadu a kafafen sada zumunta cewa Sanata Dickson ya shiga tafiyar haɗaka da ke da burin kifar da Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC a 2027.

A tsarin shugabancin PDP na ƙasa, ana kallon sanatan a matsayin wanda ke goyon bayan ɓangaren jam’iyyar da Umar Damagum ke jagoranta, wanda ya miƙa shugabanci ga Kabiru Turaki a watan Nuwamba 2025.

Dalilin daina ganin Dickson a harkokin siyasa

Sanata Dickson ya bayyana cewa ya ɗan janye kansa daga harkokin siyasa na wani dan lokaci sakamakon rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo.

Idan ba ku manta ba, mataimakin gwamnan ya rasu a watan Disamba 2025 a cikin gidan gwamnatin Bayelsa lokacin da yake shirin shiga wani taro.

Kara karanta wannan

An fadi shekarun da mulki zai yi a Kudu kafin ya dawo yankin Arewa

Jam'iyyar ADC.
Tambarin jam'iyyar hadaka, ADC Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki na janye wa daga harkokin siyasa domin girmama marigayi mataimakin gwamnan, cewar rahoton Vanguard.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana ci gaba da karɓar ta’aziyya daga abokai, shugabannin siyasa, magoya baya da masu fatan alheri daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa bayan kammala jana’iza da sauran al’adun binne marigayi mataimakin gwamnan, zai koma harkokin siyasa tare da yin shawarwari da abokai kafin ɗaukar kowane irin mataki.

ADC ta fara tattaunawa da PDP da NNPP

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ana tattaunawa tsakaninta da jam'iyyun NNPP da PDP kan yiwuwar haɗaka gabanin zaɓen 2027.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana maganar hadakar a Abuja, inda ya ce jam’iyyar na tattaunawa da NNPP da PDP.

Ya jaddada cewa abin da jam’iyyun ke dubawa shi ne yadda za a samar da shugabanci nagari, da manufofi masu ma’ana da za su inganta rayuwar talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262