Ribas: Gwamna Fubara na tsaka Mai Wuya, Azumi da Addu'a kadai Za Su Cece Shi

Ribas: Gwamna Fubara na tsaka Mai Wuya, Azumi da Addu'a kadai Za Su Cece Shi

  • Ayodele Fayose ya yi ikirarin cewa babu abin da zai ceci Gwamna Similayi Fubara daga rikicin jihar Ribas sai addu'o'i da azumi
  • Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya tuna tattaunawar da ya yi da Wike lokacin da ya halarci bikin rantsar da Simi Fubara a 2023
  • Kalaman Fayose na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Fubara da mataimakiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya tsoma baki kan dambarwar da ke faruwa tsakanin 'yan majalisar dokokin Ribas da Gwamna Siminalayi Fubara.

Fayose, wanda ake ganin yana da kyakkyawar alaka da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya ce azumi da yawaita rokon Allah ne kadai za su iya ceton Gwamna Fubara.

Kara karanta wannan

An kira sunan Atiku da aka lissafa 'yan siyasar da suka 'ruguza' jam'iyyar PDP

Tsohon gwamnan Ekiti.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose Hoto: Ayo Fayose
Source: Facebook

Abubuwan da za su ceci Gwamna Fubara

Da yake magana a shirin Politics Today na Channels, Fayose ya shawarci Fubara da ya yi sulhu da tsohon ubangidansa kuma magabacinsa, Nyesom Wike, wanda a halin yanzu shi ne Ministan Abuja.

“Sai an dage da addu’o’i domin a ceci Fubara. Azumi da addu’a ne kaɗai za su iya ceton Fubara a wannan hali,” in ji Fayose.

Mene ne ya hada Fubara da Majalisar River?

Gwamna Fubara da Majalisar Dokokin Jihar Ribaa sun fara rikici ne kan rashin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da gwamnan bai yi ba.

‘Yan majalisar sun fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa, suna zarginsa da kashe kuɗaɗen jihar ba tare da amincewar su ba.

Mafi yawan ‘yan majalisar Ribas suna biyayya ga Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, wanda ke adawa da neman tazarcen Fubara a zabe mai zuwa.

Wike ya zargi Fubara da karya yarjejeniyar sulhu da suka cimma kafin Shugaba Bola Tinubu ya dage dokar ta-baci da aka sanya a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

Fayose ya dora laifi kan Gwamna Fubara

Da yake tsokaci kan lamarin, Fayose ya dora laifin rikicin kan gwamnan Ribas, yana mai cewa Fubara bai kiyaye yarjejeniyoyin da aka cimma a Abuja ba.

Tsohon gwamnan Ekiti ya tuna yadda ya halarci rantsar da Fubara a matsayin gwamna a 2023, yana mai cewa Wike bai taɓa zato cewa Fubara zai ci amanarsa ba, in ji Daily Post.

“Ban taɓa tunanin wannan lamari zai faru tsakanin Gwamna Fubara da Wike ba. Ina zaune a kan babban tebur ranar da aka rantsar da Fubara. Na gaya wa Wike cewa ina so in faɗi abu ɗaya ko biyu don gargadin Fubara kada ya ci amanarka.
“Amma sai ya ce, ‘Kada ka faɗa, ba zai iya yin hakan ba.’ A halina na faɗin gaskiya, na fito na ce, ‘dan’uwa, ka rufe kofa, kada ka saurari mutane, jama'ar Wike ne suka kawo ka, ka zauna tare da su, kada ka nemi matsala da Wike.’”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dauki zafi, ta yi magana kan shirin tsige Gwamma Fubara daga mulki

- In ji Ayodele Fayose.

Gwamna Fubara da Wike.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Majalisa ta aika takarda ga Gwanna Fubara

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ribas ra tura takardu domin sanar da shirinta ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Majalisar ta sanar da cewa an samu nasarar mika takardar shirin tsige wa ga Mataimakiyar Gwamna, Farfesa Ngozi Nma Odu, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.

Sa’a guda bayan haka, majalisar ta sake wallafa cewa an mika wa Gwamna Siminalayi Fubara takardar shirin tsige shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262